CIBIYAR ‘YAN JARIDA TA DUNIYA (IPI) RESHEN NIJERIYA TA ZABI SHUGABANNINTA

0

CIBIYAR ‘YAN JARIDA TA DUNIYA (IPI) RESHEN NIJERIYA TA ZABI SHUGABANNINTA

Mu’azu Hassan
@ Katsina City News

Babbar Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa wadda ake kira da Turanci INTERNATIONAL PRESS INSTITUTE reshen Nijeriya, ta zabi shugabanninta a taron da ta gudanar ranar Alhamis 16/12/2021.

Taron, wanda ya gudana a dakin taro na kamfanin jaridun DAILY TRUST, ya samu halartar wasu membobin Cibiyar kai tsaye, yayin da wasu kuma suka halarta ta ‘yanar gizo daga Jihohi daban-daban da kuma kasashen waje.

Zaben an yi shi ne a karkashin Kwamitin mutane uku da ke karkashin shugabancin Malam Kabir Yusuf, Shugaban kamfanin DAILY TRUST da Kadiria Ahmad, Shugabar gidan REDIO NOW da ke Legas da dan Kwamitin Amintattun Cibiyar, Raheem Adedoyin.

An yi zaben ne ta hanyar sirri, inda Musikilu Mojeed, babban Editan jaridar PREMIUM TIMES, ya zama Shugaba, sai Malam Ahmad Shekarau na kamfanin jaridun DAILY TRUST ya zama Sakatare, yayin da Rafatu Salami ta Muryar Nijeriya (VON) ta zama Ma’aji.

Barista Zainab Musa ce ta rantsar da shugabannin bayan kammala zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

See also  ROBOTICS BOOTCAMP FOR KIDS IN ABUJA!

A jawabin amsar shugabancin a madadin wadanda aka zaba, Mojeed Musikilu ya ce, za su yi aikinsu tsakani da Allah, kuma za su kare martabar aikin jarida da kuma ‘yan jarida a Nijeriya da duniya baki daya.

Daga cikin membobin Cibiyar da suka halarci taron akwai, Malam Mannir Dan Ali; daga kamfanin DAILY TRUST, Eniola Bello; daga kamfanin THISDAY, babban Editan jaridar NEWSDAIRY, Zainab Suleiman Okino; daga BLUEPRINTs da Catherine Agbo; daga 21ST CENTURY CHRONICLE, Mr. Akinrenti da Muhammad Danjuma Katsina; daga kamfanin jaridu da mujallun KATSINA CITY NEWS, Mrs. Kadiria Ahmed; daga REDIYO NOW, Malam Kabiru Yusufu da sauransu.

Cibiyar IPI an kafa ta ne a 1950, babbar hedikwatarta tana birnin Vienna na kasar Austria.

Cibiya ce da ta hada Editoci da kuma manya da fitattun
‘yan jarida na duniya.

Makasudin kafa ta shi ne kare martabar aikin jarida da ‘yan jarida a duniya.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here