Cin Zarafin Yara Ya Zama Ruwan Dare A Najeriya

0

Daga Abdulrahman Aliyu

A wani bincike da hukumar kula da kananan yara ta duniya ta gabatar a Nijeriya, kan yadda ake cin zarafin kananan yara. Ta bayyana yadda kullum ake samun korafe-korafe na cin zarafin yara ta fuskoki kala-kala.

A binciken da ta gabatar ta bayyana cewa a Nijeriya akwai fitattun hanyoyi uku da ake cin zarafin yara, wadanda suka hada da:
Cinzarafin yara na fili, kamar a Makarantu in da ake samun korafe-korafe na muzantawa yara dalibai tsakanin malamai ko kuma tsakanin daliban da suka fi wasu shekaru. Da kuma irin yadda wasu malamai ke azabatar da yaran ta fuskar basu horo wanda ya wuce hankali.

Hukumar ta samu koke da yawa na yadda ake muzanta yara almajirai da cin zarafinsu, har ta bayar da misali da wani yaro da malaminsa ya azabatar da shi har ta kai ga an datse masa hannu.

Hukumar ta bayyana hanya ta biyu ta cin zarafin yara da ake ta fuskar yi masu fyade, wanda hakan ya zama ruwan dare har ta kai ga ana yiwa yara yan kasa da shekara daya fede a wasu yankunan kasar nan, wanda hakan ke sa ana samun Kanan yara dauke da cutar Kanjamau ba tare da sun san dalilin kamuwarsu da cutar ba.
Hanya ta uku da hukumar ta gano ita ce hana yara walwala, in da ake samun korafe-korafe musamman ga yaran da aka bari hannun kishiyoyi. Hukumar ta bayyana cewa suna samun koke akai-akai kan yadda ake azabatar da irin wadannan yara da tozartasu, tare da hana su walwala, ta sigogi kala-kala. A  fuskar wadanda ake barwa renon yara a  gida, nan ma hukumar ta koka vkan yadda take samun koke na muzantawa da kaskantarwa da ake wa yaran daga masu renon.

See also  Gwamnatin jihar Kano ta fara shirin gyara makarantu 21 a fadin jihar.

Hukumar ta yi baje kolin wasu Hotuna kala–kala masu dauke da yadda aka ci zarafin yara a Nijeriya.

Haka kuma, ta yi kira ga mahukuntan kasar nan da su tashi tsaye wajen magance wannan matsala da kuma daukar mataki mai tsanani kan cin zarafin kananan yara.
Sannan ta bayyana cewa yara suna da ‘Yanci da walwala da ya kamata a ce sun mora ba tare da an yi masu shamaki ko tsananta masu ba.
Kazalika, Hukumar ta bayyana cewa, ba zata saurarawa duk wanda aka kama da laifin muzantawa ko cin zarafin kananan yara ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here