Farfesa Sheka
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Masanin tattalin arzikin nan da ke Tsangayar Tsimi da tanadi na Jami’ar Bayero Farfesa Garba Ibrahim Sheka, ya ce cire tallafi man Fetur da karin wutar Lantanki da gwamnati ta yi shi ne ya haddasa hauhawar farashinan kayayyakin da ake fama da shi a yanzu,
Farfesa sheka ya bayyana haka ne a wata da yayi da gidan Radiyo Freedoom Kano, ya ce nan gaba ma idan gangar mai ta cigaba da hauhawa a kasuwar duniya to babu shakka mai zai cigaba da hauhawa da sai mutane sunyi mamakinsa,
Farfesa Ibrahim Sheka ya kara da cewa kasar nan ta taallaka ne kacikan akan Man fetur, wanda kuma a yanzu gwambatin tarayya ta janye tallafin da take bayarwa wanda da shi ne ake samun saukin rayuwa,
Tun yana dala arbain ya koma dala 70 to kuma yana komawa dala 70, naira 400 za mu rika sayen lita, domin su kamfanuuwan da duke saya a haka suke saya sai su sarrafa shi su kawo, idan mutum zai sa yi mai a dala 30 ya je ya sarrafa ya sayar maka da shi 140, lokaci da ya koma dala 70 shi ma ninka farashi zai yi, a haka ne kawai zai ci riba,
Farfesa Sheka ya jaddada cewa bude boda ce mafita mafi sauki da talaka zai samu sasauci ga al’amuran kasar nan.