Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus daga mukamin babban alkalin alkalan Najeriya.
A cewar gidan talabijin na Channels, Tanko ya yi murabus a daren jiya bisa dalilan rashin lafiya.
An tattaro cewa yanzu haka ana shirye-shiryen rantsar da babban alkalin kotun koli na gaba, Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya na riko.
Rahotanni sun kuma nuna cewa nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwar a hukumance.
Har sai da ya yi murabus, rahotanni sun nuna cewa Mai Shari’a Tanko Muhammed na fama da matsanancin rashin lafiya.
A makon da ya gabata ne alkalan kotun kolin su 14 suka rubuta masa wasika domin nuna rashin jin dadinsu game da yadda al’amura ke gudana a kotun.
Wasu daga cikin batutuwan da alkalan kotun suka gabatar a cikin wasikar sun hada da rashin sauya motocin da suka lalace, matsalolin masauki, rashin kula da lafiya a asibitin kotun koli, da rashin wutar lantarki.
Alkalan sun kuma koka da yadda aka kara kudin wutar lantarki, babu wani canji na alawus da zai nuna karin farashin man dizal, da kuma rashin ayyukan intanet a dakunansu.