DAKARUN DAJI SUN KAI HARI A WANI KAUYE.
Daga Taskar Labarai
A daren alhamis, Wanda yayi daidai da 26:12:2019 dakarun daji sun kai hari a wani kauyen mai suna Kwatarni dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Sun yi barin wuta kamar ana yakin kasa da kasa daga bisani suka yi awon gaba da shanu da dama. Ganin haka yasa mutanen kauyen da na makwabtansu suka bisu domin kokarin kwato shanunsu, sanadiyyar haka yasa mutune biyu suka rasa rayukansu daya dan Kwatarni dayan kuma ya fito daga wani kauye wai shi Kumumuwa, wasu Kuma sun tsira da raunuka ciki har da wanda ya samu karaya.
Amma jamian tsaro sun kai masu dauki daga bisani. Tun bayan sasancin da ake ganin an yi da maharan aka dan samu tsagaitawar kai hare-hare da Garkuwa da mutane, amma yanzu kuma abun na neman dawowa sabo, wanda ke nuna cewa kamar barayin sun yi wani shiri ne na musamman a lokacin da suka tsagaita wuta.