DAKARUN DAJI SUN KAI MUNANAN HARE-HARE A BATSARI…..sun fafata da wani matashi
Daga taskar labarai
A ranar talata 07/01/2020 da misalin karfe 11:45pm na dare wasu da ake zaton dakarun daji ne suka tsallaka gidan wani matashi mai suna Bishir dake zaune a kauyen Yar-Larba dake cikin yankin karamar hukumar Batsari, in da suka bukaci ya basu kudi, da yake a ranar ya dawo daga kudancin kasar nan wajen neman kudi (ci rani), sai yace masu shi kam baya da kudi sai masara kadai ya dawo da ita idan suna so ga ta nan su dauka.
Take su ka hau shi da sara da adduna kamar ana saran kabewa. Sun yi masa munanan raunuka, amma a haka yayi ta maza ya kwaci adda hannun dayansu shima ya kai sara ya kuwa yi sa’a ya sharbe daya daga cikinsu, ganin haka yasa suka runtuma a guje, domin su tsira.
Lokacin da jama’a suka zo domin kawo masa dauki, sun same shi cikin yanayi na rashin tabbas sakamakon fafatawar da yayi da maharan, hanji waje, fuska cike da raunuka, jini ta ko ina, amma a hakan ya bayyana wa ‘Yan uwansa cewa lalle koda ya cika to ya gane wadanda sukayi masa wannan danyen aiki (watau ya bayyana masu sunayensu da rugagensu).
Sannan ya bayar da sakunan da mutane suka bashi ya kawo ma iyalansu a gida daga inda suke neman kudi, a haka dai aka daukeshi domin garzayowa babbar asibitin Batsari, amma ina kafin a isa dashi asibitin yace ga garinku nan.
Haka kuma, a ranar laraba da misalin karfe 7:35pm, kwatsam sai ga Dakarun na daji kan babura su kimanin ashirin ko wannensu yana rataye da bindiga kirarar AK-47 suka ratso garin Wagini, daidai lokacin kuwa mutane na kokarin gabatar da sallar isha’i, wannan yasa mutane suka shiga rudani. Da isarsu bakin tashar garin kawai sai suka fara kama mutane suna umurtarsu su hau babur inda suka kama mutane guda ukku, Alh. Tanimu, Salisu Dan Kallah da Abidina Lawal Gado. Bayan sun tafi dasu zuwa wani dan lokaci, biyu daga cikinsu sun kubuta sun dawo, daya ne kawai suka samu nasarar tafiya dashi watau Salisu Dan Kallah.
A daren na laraba da misalin karfe 11:00pm, dakarun daji su ka kai hari a kauyen Salihawar Batsari mai nisan 1km daga Batsari.
Su na shiga garin sai suka fada gidan wani bawan Allah mai suna Mallam Bello Babba, suka ce masa ya basu kudi yace bashi da kudi, kafi kace kwabo sai wuf ya dauki Dan bindigar nan ya buga da kasa, wannan yasa daya daga cikinsu ya harbeshi ga cinya, can sai matarsa Hajara (Hajjo) ta fito tana yekuwar neman dauki, ganin halin da mai gidanta ya shiga, amma nan take suka harbeta da bindiga wanda yayi sanadiyar rasa rayuwarta.
………………………………………………………………………..
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta. tana da yar uwa ta turanci dake bisa www.thelinksnews.com 07043777779