A daidai lokacin da aka fara matsa kaimi na shiga harkar siyasar 2019 gadan-gadan, dan takarar majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Kawo, Hon. Alhaji Ibrahim Ammani, ya bayyana cewar rashin gamsuwa da yadda jam’iyyar APC ke gudanar da harkokin ta a jihar ne babban dalilin sa na sauya sheka daga jam’iyyar, inda ya koma PDP domin samun zarafin kawo sauyin da yake muradi.
Dan takarar ya bayyana hakan ne ga manema labarai lokacin da ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar Kaduna, domin shaida yadda ake sayar da fom na takara da PDP ta fara a talatar nan.
Hon. Ibrahim Ammani ya ci gaba da cewar tsarin tafiyar APC a jihar Kaduna ya gamu da kalubale sosai, sakamakon tauye hakkin ‘ya’yan jam’iyyar da ake yi, inda ba a bada dama ‘ya’yan jam’iyyar na zaben wakilai da kansu sai ana musu dauki dora. Alhaji Ammani ya bada misali da zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar, zaben da aka yi shi ba tare da gudanar da zaben fitar-da-gwani ba, lamarin da ya sanya ‘ya’yan jam’iyyar da dama fusata da kuma daukar matakin ficewa daga jam’iyyar zuwa easu jam’iyyu musanman PDP.
Dan takarar majalisar wanda gogaggen Dan jarida ne, ya koka dangane da irin wakilcin da mazabar Kawo ke samu a tsawon lokaci, inda ake tura wakilai masu zaman dumama kujera kawai, haka ya sanya yankin mazabar Kawo ya zama a baya wajen cigaban rayuwa.
Hon. Ibrahim Ammani ya yi alkawarin kawo sauyi da sauya fasalin wakilcin mazabar Kawo a majalisar dokokin jihar Kaduna, idan Allah ya nufe shi da zama Dan majalisar dokokin jihar a shekarar 2019, sannan yayi kira ga jama ‘ar mazabar kawo da jihar kaduna gaba daya da cewar su tashi gaba daya wajen ganin sun mallaki katin zabe na din din, domin shine makami a garesu wajen zaben shugabanni na kirki da kuma kawar da baragurbi.