DAMBARWAR SARAUTA A MASARAUTAR RIMI

0

DAMBARWAR SARAUTA A MASARAUTAR RIMI

Tun Bayan bayyana nadin Magajin Garin Iyatawa, Wanda Masarautar Katsina da ta Rimi tayi ake sa toka sa katsi tsakanin wasu masu Fada Aji a Karamar Hukumar Rimi da kuma Al-ummar Gari.

Biyo bayan rasuwar magaji garin Iyatawa da kuma dambarwar neman sarautar da aka dade ana yamutsa hazo a kanta.

An Bayyana MALAM BISHIR ABDULLAHI a Matsayin Sabon Magaji.

Kwatsam Kuma Yau an wayi Gari da wani Sabon Labari cewa Akwai Yiyuwar an Sauya Sarautar Zuwa ga HASSAN JUNAIDU IYATAWA wannan Labari Dai da Alama baizoma Mutan Gari da Dadi ba.

Malam Bishir Abdullahi, shine babban da ga marigayi magaji Iyatawa ABDULMUTALLAB JUNAIDU wanda ya rasu a watan daya wuce, kuma shine al’ummar masarautar Iyatawa musamman talakawa suke so domin ya dasa daga adalchin da mahaifin shi yake yi.

See also  SIYASA TA FARA FARAKKA 'YAN KANNYWOOD

shi Hassan Junaidu Iyatawa Kanene ga Marigayi tsohon Magajin Garin Iyatawa.

Lallai Akwai Bukatar Mai Girma Gwamnan Jahar Katsina yayi Nazari Kafin Sauya wannan Matsaya da wasu suke son yayi akan wannan Sarauta.

Allah ya zaunar damu Lafiya Amin

Copied from Muhammad Aminu Kabir

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here