DAN MAJALISAR JAHA ..YA SHA WULAKANCI A ZAKKA

0

DAN MAJALISAR JAHA ..YA SHA WULAKANCI A ZAKKA
Daga taskar labarai
Wani bidiyo da taskar labarai ta gani , wanda kuma ta tabbatar da ingancinsa.taga yadda wasu mutane suka yiwa dan majalisar jaha daga karamar hukumar safana Abduljalal iliya runka kofar raggo..suna muzanta shi
A bidiyon wanda aka ce an dauke shi ne a garin zakka ta karamar hukumar safana .dan majalisar yaje ne don neman goyon baya amma sai ya hadu da fushin talakawa.
A bidiyon munji wata murya na cewa kara tsala masa bulalar.da Zage zage marasa rubutuwa
A bidiyon an ga na tangazar keyarsa ta baya da mangarar hularsa da tunkudarsa.sannan murya na bakaken kalamai na biyowa a bayan kasan hoton
Anga lokacin da aka fitar da dan majalisar daga wajen ba hula da kyar da ban magana.
Karamar hukumar safana ta zama waje mafi zafi a siyasa a jahar katsina
Taskar labarai ta gano ko a kwanakin baya a karkashin mota cikin gareji kantoman ya boye .kafin jami an tsaro suje su ba jama a magana su fito dashi
Taskar labarai ta gano hatta dan majalisar tarayya mai wakiltar .yankin ya kasa fita yakin neman zabe
Dan majalisar Ahmad dayyabu.yana tsoron abinda zai biyo baya.don haka daga katsina yake buga waya yana yakin neman zaben sa..sai kuma ta wakilai da yake turawa.
Taskar labarai .ta gano safana na daga cikin gaba kura baya siyaki a siyasa.ga harin yan satar mutane.ga kuma zafin siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here