DAN MARNA YA BUDE DEPOT A WARRI

0

DAN MARNA YA BUDE DEPOT A WARRI
Umar Abubakar
@ katsina city news
Kamfanin Dan marna mai gidajen mai sama da Saba in a kasar nan ya bude depot ta kashin kansa.
Depot din Wanda zai zama wajen ajiye mai da dorashi bisa motocin tankuna don kaiwa wurare.
An bude depot din a yau laraba 30/6/2021.a birnin warri.kuma ma ajiyar ta mai zata iya daukar kamar lita milyan ashirin a lokaci daya.kwatankwacin tankar mai dari hudu.
Alhaji Dahiru Usman sarki shine Wanda ya mallaki kamfanin Dan marna,yanzu ya zama Dan katsina na farko da ya fara mallakar depot daga katsina.
An kafa kamfanin Dan marna a watan disamba shekarar 1997.yanzu yana da gidajen mai sama da Saba in a kasar nan.da tankunan mai da kuma dimbin ma aikata dake cin abinci karkashin kamfanin.
Kamfanin Dan marna na taimakon al umma ta hanyoyi daban daban daga cikin tsarin shi jin kai kamar yadda ake neman kamfanoni su rikayi.
@ katsina city news
Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
Www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here