Dan Najeriya ya kirkiro mutum-mutumi mai aiki da na’urar ramut na exoskeleton

0

Jaridar Hamada Blog ta wallafa Cewa Wani yaro dan shekara 17 a jihar Kano mai suna Isah Auwal Barde ya kera na’urar mutum-mutumi da ke aiki da na’ura mai suna exoskeleton.

 

Exoskeleton remote control wani tsari ne na sarrafa mutum-mutumin da mutum ke sarrafa shi ta hanyar nuna wasu sassan jikinsa.

 

Mutumin da ya kirkiro Robot Auwal-Barde ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a wata hira da ya yi da shi ranar Asabar cewa ya taso ne da sha’awar kere-kere.

 

Ya bayyana cewa ya kammala makarantar sakandire ta gwamnati (GSS) da ke Sabuwar Kofa, Kano, a shekarar 2021, kuma ya samu maki bakwai a fannin kimiyya a hukumar jarrabawar Afirka ta Yamma Wato (WAEC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here