Dan ta’adda Aleru ya Gana da Mutanan Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina.

0

Dan’tadda Aleru ya Gana da Mutanan Karamar Hukumar Faskarin Jihar Katsina.

 

Daga Wakilanmu

@Katsina city news

 

A ranar lahadin jiya 24/7/2022, Kasurgumin Danta’adda Adamu Aleru, Wanda gwamnatin jihar Katsina ke nema ruwa jallo, tun a wajajen shekarun 2019 har da alawaja ta naira miliyan biyar ga Wanda ya taimaka aka kama shi.

 

Ya zauna da Mutanan Karamar Hukumar Faskari ta jahar katsina a wani Daji kusa da garin ‘Yankara dake jihar Katsina. Zaman ya hadu mutanan garuruwa da dama, wadanka suka hado da ‘Yankara da Zagami da unguwar Barau da Fankama da Sabon layi da sauransu

 

Wadanda suka halarci zaman sun shaidawa jaridun katsina city news, zaman ya gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali da Iko da nuna isa ga Dan’tadda Adamu Aleru a cikin tsakiyar Dajin dake gabacin ‘Yankara. Tare da rakiyar mayakansa.

 

Dan’tadda Aleru ya tambayi mutanan dalilin son ganin shi da suke yi har suka aika masa. Inda suka bayyana halin tsoro da fargaba da suka shiga bayan an warware nadin da aka yi masa a Yandoto ta jihar Zamfara, da kuma kalaman gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da ta Mai magana da yawun rundunan yansada ta jihar katsina, a kan shi.

 

A nasa bayanin dan’addar ya ce ” Gaskiya ya ji dadin zuwan mutanan Kuma yana so, ya sanar da al’umma wallahi shi bai sa kowa ya kai hari ba, balle a kashe wani ko a kore dukiyar wasu ba, amma Masoyansa da basu ji dadin abin da a kai masa ba, suka huce kan Talakawa kawai”.

See also  AN KAI HARI GA MA AIKATAN KIDAYA A BATSARI JAHAR KATSINA

 

Ya kara da cewa “amma ko ni ne ko ba ni ne ba, dole ni za a ce, amma wallahi ko Allah ya sani ban ce, wani ya kai hari ba. Ni dai aka yi ma wa kuma na hakura.

 

Daga bisani ya wai ga wajen Kwamandojinsa na Daji ya ce ” daga yanzu kar wani ya sake kai hari ko ya shiga gidan wani ko a tare hanya, a kyale kowa ya je ya nemi abincinsa, hankali kwance.

 

Daga yanzu kowa ya je ya yi huldarsa Fulani da Hausawa. Haka Kuma ya yi kira ga tawagar da su kwakkwafi nasu shi ma zai kwakkwafi na shi.

 

Ya kuma kara da cewa ” gwamnatin ce bata san mu duka Hausawa da Fulani Kuma ita ke hada rigimar, don haka mu zauna lafiya da junanmu.

 

Daga nan aka yi bankwana kowa ya koma yankinsa, Kuma aka ci gaba da mu’amuloli tsakanin Fulani da Hausawa ba tare da tsangwamaba.

 

@www.katsinacitynews.com Jaridar Taskar Labarai

@www.taskarlabarai.com

The link news

@www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here