Dandazon matasa sun hau titi a Kano domin nuna ɓacin ransu sakamakon kisan wani matashi da ake zargin ‘yan sanda sunyi.
Matasan dai sun yi zargi cewa ‘yan sanda sun je sun kama wani mutum jiya da daddare a Unguwar Ƙofar Mata, inda washegari ake zargi sun kashe shi,
An tuntubi rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, sai dai ya ce ba zai iya yin magana ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto,
Masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi a kan titin Ƙofar Mata da ke ƙwaryar birnin Kano. A yanzu haka an rufe hanyar zuwa Kasuwar Kantin Kwari.
Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da aka shafe mako biyu a jere ana zanga-zangar Allah-wadai da cin zarafin da ‘yan sanda ke aikatawa a kusuan dukkanin jihohin Najeriya, abin da ya haddasa rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.