Daga Danjuma Katsina
Nasara Da Kurakuran Da Na Aikata
An rantsar da mu da qarfe biyar na marece.an zabe ni cikin murna da farin ciki,na dau nauyin anje gidan abincin Al mara I dake GRA.an ci abinci kyauta. A daren na nemo tsarin mulkin kungiyar , wanda akayi sabo, don a tsarin kungiyar ana canza mata tsarin mulki lokaci lokaci.ina da wajen kala uku,na samo sabon shafin dana fara karantawa shine, aikin ofis din mataimakin shugaba na jaha,
Sannan na duba wasu dokoki da ka idojin da kungiyar ta ginu akansu,a shafin day a shafi abinda aka zabe ni akansa.anan nagaan rubuta cewa.aikina guda hudu ne kawai,1.in taimaka ma shugaba akan duk wani aiki day a sanya ni,2 inyi duk wani aiki da kunguya ta sanya ni,3 In waklici shugaba, 4 in rike kungiyar in bayanan. A wani waje aka kara man wan aikin akace idan bisa wani dalili, shugaban ya zakuda to in zama shugaba,
Da na karanta wadannan aiyuka da aka ba wannan ofis nawa.sai nayi alkarin zan kiyaye su da kare su iya iyawa ta.na kuma sha alwashin b azan taba cin amanar wanda ya kawo nib a.da kuma ayyukanda aka dora mani.abin da na rike har zuwa karshen lokacin da aka sake zabe.kamar yadda zan kawo shi a rubuce,
Na kuma yi tunanin cewa yayan wannan kungiya mutane ne masu bsira da ilmi. Wanda zasu rika yi mana hukunci ne dai dai ayyukan da muka yi akan tsari kuma bisa adalci.don na kara shan alwashin zan yi komai a tsakani na da Allah,wa
A na wa tunanin a lokacin, idan nayi haka to bayan mun gama lokacin da tsarin mulkin ya shata mana,zan bar shugabanci kungiayar ana shaukin in ciga ba. Ko kuma ina cewa banyi ana cewa sai kayi.na kuma tsara ma kaina cewa zango daya kadai zanyi.wannan duk wani na tare dani ya san wannan matsaya tawa..
A daren da aka rantsar damu na tsara kaf,yadda zan tafiyar da rayuwa ta a shugabancin kungiyar.a taronmu na farko.wanda mukayi a gidan rdiyo, shugaban da aka zaba Abdullahi izma ya nuna,mana yadda zamu sa muhimmacin kungiyar ta cigaba a gabanmu.
Hakikia ya zo da wani irin kishi, wanda yak e son kishin ya shige mu kuma ya jagorance mu akansa.ya zo da kudurin muci gaba,ya kuma zo da niyyar ya za mu tarihin da babu wanda ya taba kafa shi tunda kungiyar tazo Katsina.
Muna shigo muna da rashin yadda da junanmu,kowa na zargin dan uwansa.don haka ma kowane taro sai an dau bayanin taron,kafin a dawo sai anzo dashi an buga an raba ma kowa kuma kowa ya tabbatar haka akayi a taron day a gabata.anba kowa ya sanya hannu, ba a kuma aikata komai sai abinda dake cikin tsarin taron,
Wannan kaida ce mai kyau, wadda gaskiyar Magana rashin yadda ta sanya muka dage ta rika tafiya a ha ka,wanda daga baya da muka fahimci junanmu,muka watsar sai da muka shekara sama da biyu bamu kara hakan ba, har aka sake zabe.kuma ba wanda ya damu ko ya taba daga kara,
Mun zo ba kudi, a lokacin kudin da ake cirewa na ma aikatan jarida daga albashinsu, aba kungiya, ba a cirewa.don haka idan aka hada sai dai duk aikin da aka ba wani daga cikin jami an, kodai wani ya ranta ayi ko kuma shi wanda aka ba, ya ranta daga aljifunsa,
Wannan ya daga hankalin IZMA,wanda ya same ni har ofis ya roke ni,in fito da hanyoyin samun kudi,don a fuskaci aikin kungiyar nan gadan gadan.Na dau masa alkawarin cewa daga lokacin har zuwa lokacin da za a samu mafita.duk abin da aka nema a wajena na kudi zan bayar.amma kaidata biyu ce a rika rubutawa.a kuma rika sanyo shi a takardar karshen taron da mukeyi don abin ya zama a bude kowanne cikin zabbabbu shugabannin ya sani.wannan daga cikin laifuka na. ina bada kudi ga kungiyar don inyi yadda naso.
Wannan kuduri nawa izma ya kawo shi a taron da muke kuma kowa yayi murna da jin hakan.mun tsara ziyarar manya,jihar da neman goyon bayan su.wanda duk mukayi a cikin nasara.ziyarar kuma ta shelanta cewa NUJ tayi sabbin shugabanni da suke niyyar kawo canji.
Duk taron da muke a gidan rediyo muke yinsa.wata ran IZMA ya sameni da safe a ofis nawa yace ya za ai mu sami wanda zai dau nauyin kama mana ofis wanda daga nan zamu rika tafiyar da al amurranmu.ya yabi hakurin yan gidan rediyo damuke taro a wajensu.yace muna masu tashi na kamaka kuma mu takura su. Amma su hakura.yace kamata yi yai muna da ofis,
Na fada masa cewa muje Alhaji bilya rimi lokacin yana mataimakin kakakin majalisa.mukaje mu biyu.muka fada masa bukatunmu.yace muna da inda muke niyyar kamawa.nace gidan rabe kaita mai taya.ginin ya kallon ofis dina. Bilya yayi hanya aka kama mana na shekara daya.wannan dauke taro da nayi sila daga gidan rediyo zuwa ofis din NUJ da aka kama na daga laifin farko da nyi ma wasu yan gidan rediyo.
Da yake ofis din yana kusa da nawa. Duk taron da za ai said an huta ofis nawa kafin a hau sama wajen taro.sai ya zama ko misali za aid a ofis din NUJ sai ace yana kallon ofis na VC. Hutawa da yadda zango a ofis nawa,dai dai daya ne daga cikin masu jagorantar NUJ a kasar nan ba suyi ba.in aiki ya kawo su, musamman lokacin kamfen na kungiyar nasa. In sunzo Katsina neman goyon baya.
Wani lokaci anan ake zama kafin a hau saman bene inda ofis din yake,wani lokaci a tsaya nan ma ayi. Taron. Wannan na daga cikin laifufukan da na yi ma wasu, aka ce na maida ofis din NUJ ofis nawa.
Duk nasarorin da muka samu.a lokacin da muna jaragoncin ya samu ne sakamakon aminci da yarda da juna dake tsakaninmu.IZMA ya san cewa idan har ya mika man amana ko wani aiki sai zan yi shi tsakani da Allah. Wannan ya sanya wani hadin kai tsakanimu.
Wanda hatta wasu shugabannin kungiyar na wajen jihar Katsina.sun fahimci wannan kuma suna jinjina mana akan haka. Misali zainab rabo ringim shugabar kungiyar mata yan jarida ta wannan shiyya ta fada cewa bata taba ganin masu hadin kai kamarmu ba. Shugaban NUJ na jihar Kaduna ma ya fadi haka.haka mataimakin shugaba na kasa na NUJ Nawannan shiyyar, da sakatarensa shehu, sun fadi. Haka. Wannan hadin kai na daga cikin laifin da akai ma wasu.wai an mallake izma kullum yana ofis nawa sai kuma yadda nace masa.
Matsalar bas wadda shugaban kwastam na kasa ya bada.anyi tarurruka sau ar ba in da shidda akan wannan KES.duk ba wanda ban halarta, ba wanda banda rubutaccen me ya faru da rawar da kowa ya taka.ni na sa hannu a madadin NUJ a rubutacciyar takardar da aka sulhunta maganar a gidan Dakta sani lugga wazirin Katsina.daga bangarensu kuma mutum biyu suka sanya Hannu.
Ni na sanya Hannu a madadin NUJ a wajen yan sanda cewa , an janye maganar. Bas din da yanzu ita kungiyar ke takama da ita.kuma ya yan kungiyar ke amfana.wanda ana bada ita aro ga duk dan kungiya day a bukata.bas na amfanan kowa.amma bakin jinin bas a kaina ta. dawo.laifin da akaima wasu me yasa aka amso bas.? Wasu kuma me yasa zan bada direban dake kula da bas? Me kuma yasa izma ya bada umurnin duk mai son aron bas ya zo waje na? ya kawo takardar bukatar haka?
Mun kawo karatun IIJ a Katsina. Dani akaje Abuja. Aka zauna day an makarantar a Katsina.da za a fara karatun,sakatare wanda a lokacin yana jarabawa a wata makaranta da yake.sai ya damka duk al amarin makarntar a wajena.a ofins dina aka ruka rijista.duk abinda ya shafi makarantar har zuwa fara karatunsu.yaran ofis dina suka rika tafiyar da lamarin.wannan na daga cikin laifin da akai ma wasu me yasa haka?karatunma ya kwace?
Duk tsawon lokacin da Aminu ahamad ayek shugabantar kungiyar NUJ ba a karbar kudin kungiya daga maiaikatan. Watau ba a cirewa daga labashi. Lokacin tsarin mulkin kungiyar ya soke a rika amsar wadannan kudade. Sai dai duk shekarra a rika biyan kudi ga uwarkungiya.da aka canza tsarin mulkin cewa a rika cire kudin daga albashi.
A Katsina a kwai kafofin watsa labarai kamarsu.ma aikatar watsa labarai.gidan rediyo da talabijin wadanda ma aikatan jaha,ana canza wancan tsarin, aka fara cire masu.nan kuma wata muhawara ta tashi. Akan yadda za arika raba kudin.kamar yadda tsarin mulki ya tsara.
Anyi ta zama.wanda daga baya aka yanke shawarar a rika ba wadanda ake cire kudaden nasu wani kaso.aka sanya waje na za a rika zuwa ana amsar wannan kason.ni za azo la rubuta takarda I n baka kamar yadda aka ce.subhannallah. wannan shima ya tayar da wata muhawarar.?ya za ai wanda shi ba a cire masa kudi,ya rika bamu kudi.?wannan aikin ma ajin jam iyya ne?
Daya daga cikin nasarar da muka samu itace.samarwa da kungiyar waje na din din.wanda aka bamu tsohuwar ginin KTTV da kuma NTA lokacin da aka bamu. An ta samun asakala tsakaninmu da hukumar Nta.wata rana IZMA ya same ni yace y azamu iya amsar ginin nan ya dawo wajenmu dari bisa dari?
Saboda duk lokacin da yayi ma Nta Magana. Sai su bashi wani labari daban.muka tsara cewa a farfado da kaddamar da kwamitin dattawan kungiyar.a kuma ginin IZMA yace ya bar man aikin akai Magana da sakatare shima ya goyi baya.
Na tsara yadda za a amshi ginin a matakai uku.lalama biyu rikici hawa na karshe.an amshi ginin amma yadda aka bi har sai da shugabar Nta ta jahar wadda mutum niyar kirkice kuma muna mutumci da ita.ta bugo man waya tana nuna man rashin jin dadinta akan wasu abubuwa da akace sun faru,wadanda duk karya ne. wasu ne a NTA din da suke jin cewa kamar ginin zai subuce hannunsu,suka kirkira, nan ma na san nayi wasu wadanda akai ma laifi.ana amsar ginin aka nemi wa zai zauna ya kula da wajen? Kyauta tunda NUJ bata da kudin daukar nauyin wani, nace ina yaran da zan tura.na tura su,wannan ma an ma wasu laifi.
A Tsawon shekaru uku nan da watanni.na zama kamar wani garuje.duk wasu abubuwa sai ace ni.sauran sun rika taka tsan tsan,ni kuma duk abin day a zo yadda ake son sahaka za ayi. Kodazai batawa wasu rai.ba ruwa na.
Hakika wata rana dana ya taba jawo hankalina.yace baba na kanzo nan ofis ina zama ina lura dayyda kake tafiyar da lamurranka.yace gaskiya kana kuskure akan yadda kake tafiyar da harkar NUJ.ka tara komai akanka. Aikin ciyaman kaine.skatare kaine . ma aji kaine.mai binciken kudi kaine,mai bicike da tan tancewa kaine.
Yace baba ka saba ma duk wata kaida da kake koya mana a yadda mutum zai kauce ma sabun sabani da ajama a. idan yana shugabanci.yace na lissafa na lissafa naga ba inda zaka iya fitar da kanka daga halin daka sa kanka.sai dai in har ba zaka sake neman tsayawa takara ba.amma in fada maka gaskiya har naji duk na tsani wannan matsayin da kake ciki.saboda sakamakonsa bai da kyau a iya hange na,
Wannan damuwa ta Muhammad wanda dalibi ne wata Babbar makaranta ana Katsina. Har sai da ya fada ma mahaifiya ta da yai man tambayar na zayyana masa daki daki cewa. Ga yadda na samu kaina har duk wannan abubuwa suka faru.na ce nima na yanke shawarar ba sake tsayawa takara.wannan matsaya ta faranta masa rai sosai, ya kuma ce wannan ya cire masa damuwar dake damunsa.
Nayi tasiri sosai a tsakanin yan kungiyar NUJ.amma a waje, ko cikin dangina wasu basu san matsayin da nake rike dashi ba.balle jami an gwamnati. Balle sauran yan cikin gari, kowa ina mua amala dashi ne a matsayin sunan da ya sanni, a kuma yadda ya sanni.
Ban taba amfani da matsayi nab a na nemar kaina wata alfarma. A duk Katsina.ba abinda zan nema ya gagare ni da matsayin da nake.akan haka na natsu bani bukatar sake tsayawa takara.
KASHI,NA UKKU YADDA NA SHIGA ZABE NA KUMA SHA KAYE..