Dr Usman Bugaje 2023: Jam’iyyar PRP Ce Mafita A Kasar nan.
Bashir Suleman
@ katsina city news
Dantakar shugabancin kasar nan da ya fito daga jihar Katsina, a Jam’iyyar PRP mai alamar makuli, Dr. Usman Baga, ya yi alkawari kawo sauyi a halin da ake ciki a kasar nan, na rashin tsaro, wanda ya zama alakakai da tarnaki ga tattalin arziki da a Jindadi da walwalar al’ummar katsinar nan.
A zantawar da ya yi da jaridun katsina city news, a wajen taron masu ruwa da tsaki da masu zaben fitar da gwani na Jam’iyyar, a ofishinta dake katsina, Dantakarar ya sha alwashin kawo manufofi ingantattun da za su maganace matsalar tsaro da farfado da tattalin arzikin nan, muddin ya samu damar yi wa Jam’iyyar takara aka kuma zabe shi a babban zabe da za a gudanar a 2023.
Ya kara da cewa Jam’iyyar na da kudurin samar da ingantaccen tsarin kan siyasar kasar nan, ta yadda ake narkar da kudade a wajen harkokin takara.
Dr Bugaje ta ci gaba da cewa dukkan jam’iyyun APC da PDP sun gaza wajen ciyar da kasar nan gaba. Ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su mara wa jam’iyyar PRP baya ta hanyar kafa gwamnati a babban zabe mai zuwa.
Dantakar ya ce, muddin ya aka zabe shi a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar, tamkar an samar da ingantacciyar hanya ce ta bunkasa harkokin noma da tattalin arziki da gina al’umma.
Ya kara da cewa a halin da ake ciki yanzu, gwamnati PRP ce ta dace da kasar nan, domin za ta bunkasa hanyoyin samar da kudade ta mayar da hankali kan haraji ba mai kadai ba.
Taron ya samu halartar dukkan Shugabannin Jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, na dukkanin fadin jihar katsina, da kuma yantakarar Gwamna guda biyu na jihar katsina.
A daukacin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu, sun yi magana ne kan abin da ke damun kasar nan, da kuma yadda za a magance shi ta hanyar kafa gwamnatin PRP, da kuma samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar tarayyar Nijeriya.
An gudanar da taron a Ofishin Sakatariya Jam’iyyar dake kan hanyar IBB, Katsina.