Inji shugaban INEC
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ta gama duk wani shiri don gudanar da zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Ondo a ranar Asabar mai zuwa, 10 ga Oktoba, 2020.
Farfesa Yakubu ya ce, “Hukumar ta shirya wa zaɓen. Yau kwana na biyu a nan Jihar Ondo ina duba shirye-shiryen da mu ka yi kuma na gamsu da abin da na gani.”
Shugaban ya bada wannan tabbacin ne a wajen wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki a wani babban zauren taro da ake kira Dome International Culture and Event Centre a birnin Akure a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2020.
Ya yi wannan bugun ƙirjin ne duk da yake an yi wata gobara wadda ta laƙume injinan karanta katin zaɓe kamar yadda aka faɗa a labarai kwanan nan.
Farfesa Yakubu ya ƙara da cewa, “Game da gobarar nan abin baƙin ciki da ta faru wadda a watan jiya ta cinye dukkan injinan mu na karanta katin zaɓe a Jihar Ondo, mun kawo isassun madadin su daga Jihar Oyo kuma mun sake saita su don zaɓen da za a yi ran Asabar. Mun yi isasshen shiri tare da Hukumar ‘Yan Kwana-kwana ta Ƙasa don tabbatar da cewa irin wannan abu bai ƙara faruwa ba.”
Yayin da ya ke lissafa irin natakan da aka ɗauka don samun gudanar da zaɓen ranar Asabar cikin nasara, Farfesa Yakubu ya ce, “Mun ɗauki dukkan ire-iren ma’aikatan wucin gadi da mu ke buƙata, mun horas da su, mun tantance su, saboda zaɓen. Mun kai kayan aiki marasa hatsari zuwa dukkan Ƙananan Hukumomi guda 18 na Jihar Ondo. Mun gargaɗi ma’aikan mu (na wucin gadi da na dindindin) da su yi aiki bisa ƙwarewa kuma ba tare da wariya ba wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora masu. Ana ci gaba da aikin wayar da kai da faɗakar da masu zaɓe.
“Mun gama shirin kwasar ma’aikata da kayan aiki zuwa wuraren zaɓe a dukkan rumfuna 3,009 da mazaɓu 203 da ke faɗin jihar.
“Yau da yamma, Babban Bankin Nijeriya zai kai dukkan kayan aiki masu hatsari zuwa reshen sa na Akure.”
Ya ce: “Mu na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa tare da hukumomin tsaro a ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomi kan Tsaro a Zaɓen (Inter-Agency Consultative Committee on Election Security, ICCES) don tabbatar da yin zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsaro a ranar 10 ga Oktoba.”
Ya miƙa godiya ta musamnan ga dukkan hukumomin da ke cikin ICCES, musamman jagorar hukumomin, wato rundunar ‘Yansandan Nijeriya, saboda yadda su ke ci gaba da bada goyon baya da aiki cikin ƙwarewa a lokacin da ake shirin zaɓen.
Shugaban na INEC ya kuma faɗi cewa: “Tun daga lokacin da Hukumar ta fitar da jadawalin ranaku da ayyukan zaɓen gwamna na Jihar Ondo watanni takwas da su ka gabata a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, mun yi ta aiki tare da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su a wajen tarurruka daban-daban. Kuma mun yi ta musayar ra’ayoyi da hukumomin tsaro a mataƙin ƙasa da na jiha.
“Mun yi tuntuɓa tare da neman goyon baya da addu’ar Majalisar Sarakuna ta Jihar Ondo. Mun zauna da shugabannin addini, ƙungiyoyi masu zaman kan su da kuma kafofin yaɗa labarai.
“Mun tattauna da Kwamitin Wanzar da Lumana na Ƙasa (National Peace Committee) da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abdulsalami A. Abubakar, GCFR, wanda ya gayyato jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar don su zauna su rattaba hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya a nan Akure gobe.”
Farfesa Yakubu ya ce, “Babban burin mu shi ne mu tabbatar da cewa zaɓar wanda zai zama Gwamnan Jihar Ondo gaba ɗaya ya na hannun masu zaɓe.
“Ina so in tabbatar wa da dukkan masu zaɓe cewa kowace ƙuri’a da za a kaɗa za ta yi tasiri kuma wanda jama’ar Jihar Ondo su ka zaɓa kaɗai ne zai kasance sakamakon zaɓen.
“Ina so in tabbatar wa da jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su cewa za mu ci gaba da kasancewa masu bin dokoki da ƙa’idojin aikin mu.
“Bari in ƙara tabbatar wa da dukkan masu ruwa da tsaki cewa Hukumar Zaɓe ba za ta ɗauki kowane irin mataki don ta daɗaɗa ko baƙanta wa wata jam’iyyar zaɓe ko ɗan takara ba.
“Hukumar ta yi nazarin yadda ta gudanar da zaɓen gwamna kwanan nan a Jihar Edo. A shirya mu ke mu ci gaba da inganta aikin mu. Saboda wannan dalilin, mun gano wurare 16 da ke buƙatar inganta aiki, waɗanda su ka haɗa da kayan aiki, ɗaukar mataki kan injin zaɓen da ya samu matsala cikin gaggawa a Ranar Zaɓe, matsalar sayen ƙuri’a a lokacin zaɓe, da kuma bin dokokin kare kai daga cutar korona.
“Don haka, mun ɗauki hayar motoci da jiragen ruwa na sufuri don kai da kawon kayan aiki a wurare masu tsandauri da kuma waɗanda ke yankunan da ruwa ya ke.
“Mun ƙara ɗaukar ma’aikatan wucin gadi guda 104 don bada tallafi a yankunan da masu zaɓe su ka yi rajista don su yi aikin gaggawa kan injinan karanta kati a Ranar Zaɓe.”