DUK MINTI DAYA MUTUM 6 NE SUKE SHIGA TALAUCI A NIGERIYA

0

DUK MINTI DAYA MUTUM 6 NE SUKE SHIGA TALAUCI A NIGERIYA

Da Ibrahim Hamisu, Kano

Masanin tattalin arziki nan na Nigeriya kuma malamin a kwalijen Sa’adatu Rimi da ke Kano Dr. Abdussalam Muhd. Kani ya ce duk a cikin minti daya ‘yan Nigeriya shida ne ke fadawa cikin talauci, inda muka zama lamba daya a wajen talauci a duniya,

Dakta Abdussalam ya ce bincike (Poverty clock) ta tabbatar da cewa mutunen duniya gaba daya mutum Biliyan 8 ne, matalauta kuma a duniya Biliyan 3 ne da Miliyan 500, ya zuwa yanzu Matalauta a Nigeriya ya kai mutum miliyan 90 don haka matalautan a Nigeriya sun fi mutanen kasar Jamus yawa domin mutanen Jamus mutum miliyan 83, matalautan Nigeriya sunfi kasar Turkiyya yawa domin mutanen kasar Turkiyya su miliyan 82 ne,

A wata hir da ya yi da shirin ‘Daurin Boye’ na Dala Fm Ya kara da cewa “duk duniya Nigeriya ce ta fi kowace kasa yawan wadanda ba sa zuwa makaranta, domin bincike ya tabbatar da cewa yaran da basa zuwa makaranta a yanzu sun kai miliyan 10.5,”

See also  AN HARAMTA KAMA KARUWAI A NAJERIYA

Hakazalika bincikin ya kara da cewa duka inda kaga mutum 4 a duniya da basu je makaranta ba, to daya dan Nigeriya ne, shi fa wannan maganar rashin zuwa makarantar mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ms ya fada da bakinsa.

Dr. Kani ya karkare da cewa idan ka ce me ya janyo mana talauci a Nigeriya “za ka iya cewa Rashin iya shugabanci, rashin iya tasarufi da kudin alumma ta inda bai kamata ba, Rasawa da cin hanci, cost of Government kudade da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati da sauransu”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here