FARFESA MAQARI YA AJIYE AIKIN KOYARWA A JAMI’A
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Babban limamin masallacin birnin tarayya dake Abuja Farfesa Ibrahim Ahmad Said Maqariy ya ajiye aikinsa domin maida hankali wajen hidimtawa Addini.
Sheihk Makari da ya shafe shekaru ya na aikin koyarwa a jamiar Bayero ta kano, ya ce ya dauki wannan mataki ne domin yana daya daga cikin makarfinsa, domin tun bai wuce shekara 20 ba ya ke fatan ya daina aikin Gwamnati,
Farfesa Maqari ya kara da cewa ” Alhamdulillah da na bar aikin albashi da kaina da karfina, Allah ya albarkaci abinda zai biyo bayana”
Tuni dai Jami’ar ta Bayero ta amince da ajiye aikin malamin, a wata takarda dake dauke da amincewar hukumar makarantar.