Fasa kwaleben Giya a Kano; Hukumar Hisba na shan caccaka
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta yi gargadi ga masu caccakarta a kafafen sada zumuta na zamani musamman daga kudancin Nigeriya, saboda wai ta fasa kwalaben giya, da kudadensu yakai a kalla naira miliyan 200,inda su suke ganin asara aka yi,
Wanda hukumar Hisbar ta ce indai kamen giya anan jihar kano ne to yanzu aka fara, tunda dai ubangiji madaukakin sarki ya ce ‘ ita giya da shanta da dakonta da kuma sayar da ita duk haramun ne,
Babban kwamandan Hisba ta jihar Kano Muhammad Harun Ibn Sina ne bayyana haka ga manema labarai inda ya ce wannan caccaka da ake yi masu a social Media kara masu kwarin gwiwa ta ke yi, kuma in dai fasa giya ne to yanzu aka fara,
Ya kara da cewa ” Mu a jihar Kano yanzu muka fara don me zamu tsorata mun gani a kafofin sadarwa an samu comment sama da dubu 10 suna ta caccakarmu, kuma wallahi wannan yana daya daga cikin abuwan da Allah ya ke taimaka mana a jihar Kano”
Indai baa manta ba, a satin da ya gabata ne hukumar Hisba ta jihar Kano ta lalata giya wacce a akallah ta kai miliyan 200 wanda ya jawo cece ku ce a fadin kasar nan.