FIM DIN JUYIN SARAUTA (PALACE COUP) YA LASHE SAMA DA MILIYAN TALATIN- BALARABAT RAMAT

0

A ranar  talata aka yi bikin kaddamar da fim din Juyin Sarauta aa dakin taro na Meena Event da ke titin Lugard kusa da gidan gwamnatin jihar Kano.

Manyan mutane da dama sun halarci wannan biki sannan sun kaddamar da shi a wannan rana, babban mai kaddamarwa wanda Ya kasance dan majalisar Kiru da Bebeji  Hon Abdulmuminu Jibril Kofa ya kaddamar da shi akan kudi dubu 250 sai kuma gwamnatin jihar Kano wanda ta samu wakilci shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano Malam Isma’ila Na’abba Afakallah wanda ya sayi kwafi daya a madadin hukumarsa kan kudi naira 100 mutane da dama sun sayi nasu kwafin.

Wanda ta rubuta labarin fim din ta kuma dau nauyi hajiya Balaraba Ramat Yakubu tace fim din ya lashe sama da naira miliyan talatin a lokacin da ake yinsa.

Juyin Sarauta fim ne da aka shirya kusan shekaru uku (3years) da suka gabata, fim din yana bayar da labarin shekaru dari(100years) da suka gabata game da sha’anin labarin wata masarauta da ke garin Jadarwa, kafin shirya fim din sai da aka gina birnin da za a yi shi a cikin kauyen Iyatawa cikin garin DanHassan karamar hukumar Bunkure jahar Kano.

See also  BIDIYO

Ana sa ran fim din shi ne na farko a tarihin masana’antar shirya finafinai ta Hausa a duk fadin Afrika ta yamma (Kannywood) wanda ya samu tsaftar dauka da rubutu tare da bayyana asalin tsarin gidan sarauta da kalubalen da ake fuskanta a lokacin da sarki ke gabatar da sha’anin mulkinsa, da kuma yadda halin matan sarki ke kasancewa wajen son ‘ya’yansu su yi sarauta.

Daukar Nauyi: Balaraba Ramat Yakubu
Shiryawa:Ado Ahmad Gidan Dabino MON
Bayar da Umarni: Falalu Dorayi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here