“GASKIYA DA RIKON AMANAR SHUGABA BUHARI NE YA SA HAR YANZU NA KE A APC”– Inji Nuhu Abdullahi
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Jarumi a masanaantar Kannywood Nuhu Abdullahi ya bayyana cewa har yanzu yana goyon bayan jam’iyyar APC saboda kaunar da ya ke wa shugaba kasa Muhammadu Buhari saboda gaskiyarsa da amana wajen shugabantar al’umma.
Nuhu Abdullahi ya bayyana haka ne a kafar yada labarai ta BBC a shafinta na Instagram, ya ce yana da kwarin gwiwa akan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ke kamanta adalci a rayuwarsa,
Da aka tambayeshi ko kwalliya ta biya kudin sabulu? Nuhu ya ce Shi kansa shugaba Muhammadu Buhari ba zai taba jin dadin abubuwan da ke faruwa ba na matsalolin tsaro ba, saboda haka, saboda talakawa ya kamata su taimaka da addua da ba zagi ba.
Haka kuma ya kira ga Jamian tsaro da su kara kaimi wajen nemo bayanai akan hakikanin wajen da ake samun baraka domin daukar matakan da suka kamata, tare da samun hadin kan al’umma da masu ruwa da tsaki.