Gurguwar Shawara ce rufe Makarantu da wasu Gwamnoni su ka yi-

0

Gurguwar Shawara ce rufe Makarantu da wasu Gwamnoni su ka yi– Farfesa Malumfahi wasu

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Malamin Jamiar nan kuma Masanin halayyar dan adam na jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi ya ce gurguwar shawara aka baiwa gwamnoni kuma wannan abin takaici ne na rufe maarantu a wasu jahohi,

Ya ce “Wannan sabon hukunci na rufe makarantu da ya shafi Kano Kaduna Katsina Jigawa Zamfara da aka zartar akwai kusure a ciki kuma akwai matsala a ciki, idan saboda tsaro ne aka zartar da wannan hukunci hakika wadanda suka baiwa wadannan Gwamnoni shawara sun yi kuskure a ciki,

A wata hira da yayi da manema labarai Farfesa ya kara da cewa “wannan ya nuna rashin ingantacce shugabanci da rashin kishin jamaa, maana kenan gwambati ta ga za ba za ta iya kare rayukan wadanan yara ba, da lafiyar su, ka da fa a manta idan yaran nan sun koma gida, abinda ake so iyayen na su su yi shi ne su kare yayansu?”

See also  Zaben fidda gwani a Zamfara: INEC ta bayyana Ibrahim Tudu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben

Masharhanta a Arewacin kasar na Allahwadai a kan wannan matakin gaggawa da wasu gwamnonin suka dauka na kulle makarantu, wanda wasu ke ganin akwai siyasa a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here