Gwambatin Jigawa ta biya hakkokin ‘yan Fansho
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwannatin Jihar Jigawa ta biya hakkin ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma wadanda suka mutu, hakkokin da adadinsu ya kai sama da naira biliyan 1 da miliyan 84, a matakan jiha da kananan Hukumomi da suka kai mutane 530.
Sakataren zartarwa na hukumar adashin gata ta jihar Jigawa Alhaji Hashim Ahamad Fagam ne ya bayyana hakan a taron manema Labarai jin kadan fara biyan kudaden a ranar Litinin din nan.
Ya kuma bukaci wadanda suka yi ritaya da sukai rahoton duk wani maaikaci da yayi yinkurin karbar na goro domin yi masa jagoranci.
Jaridar Taskar Labarai ta ruwaito cewa Allhaji Hashim Ahmad ya bayyana jihar Jigawa a matsayin wacce ke sahun gaba wajen biyan kudaden fanshon a kasar nan.
Sannnan ya bayyana wannan nasarar da hukumar ke samu sakamakon irin kulawar da gwamnatin Jigawa karkashin jagorancin gwamba Muhd Badaru Abubakar.