GWAMNA GANDUJE YA BUDE SABON OFISHIN MA’AIKATAR ADDINAI

0

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon ginin ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya ce ma’aikatar ita ce za ta rika kula da hukumomin da ke kula da harkokin addinin musulunci da kuma inganta mu’amala tsakanin mabiya addinin musulunci da wadanda ma ba musulmi don wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Gwamnan ya ja hankalin ma’aikatan da za suyi aiki a sabuwar ma’aikatar, da suyi aiki tukuru bisa jajircewa da rikon amana, don tunkarar matsalolin da suka shafi bangaren.

Da yake jawabi tun da fari kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci Dr. Muhammad Tahar Adam, ya bayyana cewa shakka babu ma’aikatar za ta taimaka wajen kawo ci gaba ta fuskar addinin musulunci da kuma bunkasar ilmin addinin da dai sauran su. Sannan ya tabbatar da cewa maaikatar za ta hada kai da dukkanin malamai na kowace fahimta domin maaikatar ita ce mabubbugarsu kuma nan ne mashayarsu,

See also  “EACH TERRORIST AND EACH BANDIT WILL BE HUNTED AND PURSUED AND SPOKEN TO IN THE LANGUAGE THEY UNDERSTAND” - Buhari 

An dai kirkiri wannan maaikata ne a watan Nuwanban 2019 bayan dawowar Gwamna Ganduje zangon mulki karo na biyu, da nufin kawo sauyi ta yadda ake tafiyar da harkokin addinin musulunci dama jihar Kano ba ki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here