GWAMNA GANDUJE YA KAFA KWAMITI KAN YARAN KANO DA AKA SACE

0

GWAMNA GANDUJE YA KAFA KWAMITI KAN YARAN KANO DA AKA SACE

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamn Dr Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya kafa kwamitin da zai hada rahoto kan matsalar satar yara da aka samu a kwanakin baya.

Gwamna ya kafa kwamitin ne tare da baiwa ‘yan kwamitin takardun fara gudanar da aikin a yau Asabar, yana mai cewa, mambobin kwamitin da suka tattara bayanai da alkaluman yaran da aka sace din za su cigaba da sanya ido kan aikin Sabin kwamitin.

Da yake jawabi jim kadan bayan karbar takardar kama aiki, shugaban kwamitin Justice Wada Umar Rano ya ce, za su yi tsayin daka wajen magance matsalar satar yara a jihar Kano musamman wadanda ake kaiwa jihohin kudancin kasar nan.

See also  HOTUNAN MAHADI SHEHU A WAJEN YAN SANDA

Mutanen da za su dafa masa wajen gudanar da ayyukan kwamitin sun hadar da shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa NUJ shiyyar Kano Kwamared Abbas Ibrahim da Malam Ibrahim Abubakar Tofa, da wakilin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abubakar Umar shika, da sauran su.

A ‘yan shekarun baya ne dai aka yita samun batan kananan yara a wasu unguwannin jihar Kano, inda daga bisani aka fara gano yadda ake sacewa tare da sayar da yaran a jihohin kudancin kasar nan inda ake sauya musu addini da yare.

To sai dai kuma bayan fara gano su din ne kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar ceto wasu daga cikinsu har ma aka sada su da iyayensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here