GWAMNA GANDUJE ZAI JAGORANCI KWAMITIN YAKIN NEMAN ZABE EDO
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne zai jogoranci kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar edo kamar yadda
jam’iyyar APC mai mulki ta sanar a safiyar yau.
Kwamitin mai kunshe da mambobin 49 zai yi aiki wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a cewar sanarwar da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai na kasa Yekini Nabena.
Gwamnan Jihar Imo Senata Hope Uzodima ne zai kasance mataimakin Ganduje, sai kuma Honourable Abbas Braimoh a matsayin sakataren kwamintin yakin neman zaben.
An kafa kwimitin ne dai bayan amincewar shugabanta na riko gwamanan jihar Yobe Mai Mala Buni a zaben da ake sa ran gudanarwa a ranar 19 ga watan Satumba 2020.
A ranar Litinin 6 ga watan Yuli ne dai, jam’iyyar za ta kaddamar da soma aikin kwamitin a babban birnin tarayya Abuja.