GWAMNA MASARI: TSAKANIN MATSIN ‘YAN BOKO DA TAUSAYIN TALAKAWA

0

GWAMNA MASARI: TSAKANIN MATSIN ‘YAN BOKO DA TAUSAYIN TALAKAWA ~~~Kulle Katsina Don Cutar Coronavirus

Daga Danjuma Katsina

Tabbas gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari na fama da matsi daga masana da ‘yan boko kila ma har daga Abuja akan ya kuble Katsina ba shiga ba fita kowa ya zauna a gida koda kuwa baya da ruwan sha saboda tsoron wannan annoba ta cutar Coronavirus.

Masu wannan matsin mafi yawansu na zaune ne a wajen Katsina, kuma suna da abincin shekaru in har ma sun amince ba zasu fito ba, wasu ma da ace kofa bude take da yanzu sun Lula basu a kasar.

Tabbas abin da gwamnan ke tunani wane hali Al’umma zasu shiga a yanayin da muke ciki wanda hatta ruwan sha sai masu bukata sun fita sun nema?

Hausawa na cewa da na gaba ake gane zurfin ruwa, labarai nazo mana wasu ma har da hoton bidiyon na bala’i da kuble wasu jihohin ya jawo in da mutane suka fara tawaye wasu ma suka zama yan fashin kayan abinci da rana tsaka.

Gwamnan Katsina Masari, kamar yana cikin zuciyar mutane yana tunanin wane hali da mafi yawa za su shiga in ance a zauna a gida kar ka fito sai dole, yara nawa zasu kamu da cuttukan sanadin yunwa? Magidanta nawa zasu shiga hali oni ya su.? Fitina nawa za a fada? Me ke faruwa a wasu yankunan da aka kuble?

‘Yan boko da wasu masana na ta kiran a kuble a kuble a kuble, wasu masu yekuwar nan wasu ko shinkafa basu ci, sai abincin gwangwani da na kwalaye sun shake buhunnan a dakunan ajiye abincinsu kuma ba a zuwa gidansu sai sun baka lokaci.

Kuble gari ba shiga ba fita bala’i ne, a yanayi da yanki irin na kasarmu wanda kowa tasa ke fitar da shi, kuma a ganina zai zama fitina fiye da Coronavirus.

Matakai Wanda gwamnatin Katsina ta dauka shi ne dai-dai, farko ilmantar da Kan jama a ba dare ba rana akan cutar da yadda zaka kare kanka.

Katsina ce tafara wannan tsarin ta kafa kwamitin dake aiki ba dare ba rana. Ina amfanin a kuble ka a gida ba ilmin kariya? Na biyu kuble duk yankin da taba bulla kawai, kamar yadda hadisin Manzon Allah ( SAW) yazo da shi. Misali yadda aka yi ma garin Daura, nan ta fito nan ake son tsaida ta kar ta yadu, amma annoba ta bayyana a Daura ka kuble garin Damari ina hikima da basira take?

See also  An Gano Harsashi A Cikin Kwakwalwar Shaikh Ibraheem Zakzaky

A kasar Chaina in da cutar ta faro, basu kuble kasar su ba, amma suna rufe inda abin ya faru ne sannan kuma sun dau matakan wayar da kan jama’a, yanzu sun iya taka ma cutar burki.

Yadda gwamnatin Katsina tace, duk inda abin ya bayyana za a kuble yankin don hana yaduwar ta yayi daidai.
Fatan mu hikima bata kare ma Dan adam, gwamnatin mu ta fito da hanyoyin ga jama’a su dau matakan kiyaye wa da kariya ba tare da an kai ga cewa kowa ya zauna gida ya gane ba, su kuma mutanen su bi da aikin da duk shawarwarin da za a basu.
Sai kuma matakan hana baki shigowa domin tabbas baki da wadanda ke tafiya su dawo suke yada ta. Kalli jahar Borno da yobe da yake ana tsoron zuwansu kun ji cutar ta bulla?

Tabbas, cutar nan gaskiya ce, kuma tana barna in aka yi sakaki amma in an kiyaye tana tsayawa. Kamar yadda wasu kasashen suka iya nasarar rage ma barnar ta karsashi, saboda matakan gwamnati da biyayya ga ‘yan kasa.

In aka kai kuble wa ba abin da gwamnati zata iya yi maku na abinci sai abin da zai baku haushi kamar yadda muke gani a wasu jihohin da aka kuble.

Jihar mu na cikin tsaka mai wuya ‘yan boko da wasu masana na matsama gwamnan ya kuble ta, shi kuma ga alama yana tausayin halin da jama’arsa zasu shiga. Allah kawo mana karshen wannan annoba.

Danjuma Katsina. wakilin wasu jaridu ne a Katsina kuma shi ne ke wallafa jaridun nan guda biyu dake bisa yanar gizo. Jaridar Taskar Labarai dake a www.taskarlabarai.com da kuma The Links News www.thelinksnews.com. Kira ko WhatsApp 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here