GWAMNATIN GANDUJE ZA TA FARA GWAJIN MIYAGUN KWAYOYI GA MASU MUKAMAI

0

GWAMNATIN GANDUJE ZA TA FARA GWAJIN MIYAGUN KWAYOYI GA MASU MUKAMAI

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ana shirin yi wa duk masu rike da mukaman siyasa, ma’aikatan gwamnati da dalibai gwajin dole na miyagun kwayoyi a jihar.

A wata takarda da kwamishinan yada labarai na jiha, Muhammad Garba, ya fitar a yau Juma’a,

A yayin jawabi a ranar yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi na duniya, Garba ya ce za a fara gwajin dole daga cibiyar kula da magunguna.

Gwamnatin Ganduje na kokarin gani ta yaki safara tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi. Saboda haka ne ta kafa kwamitin yaki da wannan muguwar dabi’a a jihar.

Muhd Garba ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaki da miyagun kwayoyi, wanda yake kamawa tare da kwace miyagun kwayoyi, kuma ya kama na miliyoyin nairori,

See also  Shugaba Buhari ya karrama Alh. Dahiru Bara’u Mangal da lambar yabo ta (CON).

Ya yi kira ga jama’a da a dage wurin wayar da kan matasa a kafafen sada zumuntar zamani don su gane hadurran da ke tattare da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da ta’ammali da miyagu kwayoyi da safararsu a fadin duniya,

Taken taron na bana dai shi ne: kokari wurin wayar da kai tare da ilmantar da jama’a don su gane matsalolin kwayoyi ga al’umma baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here