Gwamnatin Kano ta dauki nauyin sanya Kofi duk shekara akan Harshen Hausa

0

Gwamnatin Kano ta dauki nauyin sanya Kofi duk shekara akan Harshen Hausa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin sanya kofin gasar kacici-kacici ga manyan makarantun jihar akan harshen Hausa duk shekara,

Mataimakin gwamna Kano Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana a taron makala da kacici-kacici da kungiyar Daliban Hausa ta Nigeriya ta shirya a Jamiar Bayero Kano jiya Alhamis, ya kara da cewa a wannan lokaci da wasu yaruka ke zagwanyewa gwamnatin kano za ta yi iya yinta ta ga ta tallafawa harshen Hausa, kuma ya ce tun kafin shekara ta yi gwamnatin Kano zata kawo kofin ga Jami’ar Bayero.

A makalarsa mai taken “Harshen Hausa jiya da yau: Kalubale da Madosa” Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Jami’a Danfodiyo da ke Sokoto wanda shugaban Cibiyar nazarin harsunan Nigeriya da fassara da hikayoyi na Jami’ar Bayero ya wakilta, ya ce harshen Hausa ya yi dacen da samun gudunmwa daga sassa daban-daban ta yadda zai iya fuskartar kowane irin kalubalen a kowane zamani.

Ya kara da cewa tun kafin mulkin mallaka a Nigeriya turawa suka bayyanar da shaawarsu ga Hausa tun a shekarun 1840. Inda a shekarar I843 Bajamushe Fredrick Schon mai hidimar ayyukan mishen ya fara rubuta Hausa ta hanyar amfani da rubutun boko, mai suna Magana Hausa.

See also  FCE Kano ta sanar da ranar dawowa Makaranta

Nura Sulaman Janburji wanda shi ne Sarki kungiyar Daliban Hausa ta Nigeriya ya ce makasudin shirya taron shi ne domin sakawa yanuwanmu al’umma kishin Hausa domin ance kowa ya bar gida gida ya barshi,

Makarantun gaba
da sakandire18 ne dai suka suka shiga Gasar, inda kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayya FCE ta leshe gasar a matsayi na daya, da kyautar dubu 500. Jami’ar Bayero ta Kano mai masaukin baki ta zo ta biyu da kyautar dubu 300 , yayin da Kwalejin sharia da addinin musulunci (Ligal) ta zo a matsayi na uku da kyautar dubu 200.

Taron dai ya samu halartar manyan baki na ciki da wajen jihar Kano da suka hada da yan Fim da Mawakan Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here