Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce tuni ta fitar da naira miliyan 880 domin gyaran makarantun a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.
Jawabin haka ya fito ne daga mataimakin Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya wakilci gwamna Ganduje, ya bayyana hakan a yau lokacin da yake bude taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki dangane da bude makarantu, da ma’aikatar ilimi ta kasa ta shirya da hadin gwiwar UNICEF.
Taron da hada masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi zai tattauna ne game da irin shirye shiryen da akayi dangane da komawa makarantun cikin Yanayin mai kyau tare da samu kariya daga cutar sarkewar numfashi ta Korona.
Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnarin Kano zata cigaba da feshin magani a makarantun jihar Kano domin Kare dalibai daga kamuwa da cutar Korona.