GWAMNATIN KANO ZA TA DAUKI MALAMAI DON KARANTAR DA ‘YAN MATA

0

GWAMNATIN KANO ZA TA DAUKI MALAMAI DON KARANTAR DA ‘YAN MATA

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta fara shirye-shiryen daukar malamai guda 2000 domin aikin karantar da dalibai a makarantun ’yan mata da ke fadin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Malam Sanusi Kiru ne ya bayyana kudirin gwamnatin na daukar malamai dubu biyu yayin da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wata gidauniyar tallafawa ’ya’ya mata (AGILE).

A cewar Kwamishinan, manufar shirin daukar malaman shi ne cike gibin da ake da shi tare da bunkasa harkokin ilimi musamman na yara mata a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Kwamishinan yana cewa wannan shiri na hadin gwiwa ne tare da wasu jihohi bakwai da Gwamnatin Tarayya da kuma Asusun Bankin Duniya.

Jihohin sun hada da: Kano da Kaduna da Katsina da Kebbi da Filato da Ekiti da kuma Borno.

See also  BAI KAMATA BA DUKAN MATA

Sanusi Kiru ya ce, tuni gwamnatin jihar Kano ta fara gina kanana da manyan makarantun sakandire guda 120 a fadin jihar tare da tanadar motocin bas-bas da za su rika zirga-zirgar daukar dalibai mata ’yan makaranta a kwaryar birnin jihar.

Ya tabbatar da cewa Gwamnati ta biya wa dalibai mata kimanin 489 kudin jarabawar kammala babbar sakandire ta NECO, da kuma ware naira biliyan 4 don ciyar da dalibai mata ’yan makarantun kwana a fadin jihar.

Kwamishinan ya kara da ce wa, bunkasa ilimin yara mata na daga cikin manufofin gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje wanda ya ce yana ci gaba da aiki tukuru ba dare ba rana don ganin an ilimin yara mata a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here