Gwamnatin Katsina ta sanya hannu kan wata yarjejiniya da wani kamfanin kasar India mai suna Contec Global Agro Limited

0

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanya hannu kan wata yarjejiniya da wani kamfanin kasar India mai suna Contec Global Agro Limited domin tayar da kamfanin NEEMPRO mallakin jihar Katsina domin yaci gaba da aiki kamar yadda aka kafa shi.

Wannan yarjejiniya ta ba wannan kamfani damar tayar da wannan kamfani tare da inganta shi ta hanyar tabbatar da yana samar da duk sinadaran da aka kafa shi domin su, wanda suka hada da takin zamani, Mai na bedi da makamantansu su.

Da yake sa hannu a madadin Gwamnatin Jiha, Kwamishinan Ciniki da Masana’antu Alhaji Mukhtar Gidado AbdulKadir ya bayyana cewa tayar da wannan kamfanin yana cikin alwashin da Gwamnatin Jiha karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari tasha na tayar da duk kamfanonin Gwamnati da suka mutu tare kuma da samar da sababbi.

Ya kara da cewa habaka bangaren kamfunna da masana’antu zai samar da karuwar ayyukan yi musamman ga matasa da samun karuwar kudin shiga ga jiha wanda zai rage dogaro ga asusun Tarayya.

A nashi bayanin, Shugaban kamfanin Contec Global Agro Limited Mista Thomas Chackunkal ya bayyana cewa jajircewa da kuma nuna damuwa da Kwamishinan ya nuna wajen ganin an tayar da kamfanin ya kara masu kwarin guiwar shiga wannan yarjejiniya da Gwamnatin Jiha.

See also  WATA SHARI A DA AKAYI A SHEKARAR 1950 A KATSINA

Da yake godiya ga Gwamnati kan wannan dama da aka basu, Mista Chackunkal ya bayyana cewa ba da jimawa ba za su tabbatar da duk bangarorin kamfanin sun ci gaba da aiki kamar yadda ya kamata.

Ya kuma kara da cewa a shirye da su rika kula da duk itatuwan bedi da suke fadin wannan jiha, za kuma su bullo da wani shiri da zai zaburar da al’umma wajen dasa bedi tare kuma bada tabbacin za su bada tallafi ga wadanda za su shiga wannan harka ta shuka bedi tare da saye diyan a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A karshe ya roki Gwamnatin Jiha ta hannun Kwamishinan da ta basu dama su kafa kamfanin samar da taki ta hanyar amfani da sinadaran dake jikin tsirrai (Biofertiliser).

Wannan kamfani dai, Marigayi Gwamna Umaru Musa Yar’adua ya gina shi a cikin shekarar 2007 ya fara aiki na wani dan lokaci daga bisani saboda matsaltsalu da suka addabe shi sai aka rufe shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here