Gwamnatin zamfara bazata lamunci watsi da ka’idojin aiki ba—- Matwalle
Daga Shu’aibu Ibrahim gusau
Gwamnatin jihar zamfara ba za ta lamunci duk wani nau’i na sasantawa ko kuma yin watsi bin ka’ida da bin doka da oda ba.
Gwamna Bello muhammad matawalle ya bayyana haka ne yayin rantsar da masu ba shi shawara na musamman guda biyar da manyan sakatarori na dindindin a gidan gwamnati jihar dake Gusau.
Gwamnan ya ce tun daga wannan lokacin an kafa ofishin bin ka’idoji domin bunkasa tabbatar da gaskiya da rikon amana saboda gwamnati ta zabi hanyar gudanar da mulki na zamani
Ya bayyana cewa ofishin da ke bin ka’idoji zai kasance tare da kwararrun Ma’aikata don tabbatar da kaucewa cin hanci da rashawa da rashin da’a, a aikin gwamnatin.
A kan sabbin shugabannin da aka rantsar, gwamnan ya bukace su da su kare matsayin Majalisar Zartarwa ta Jiha, wajen kara daraja da kwarjinin.
Ya ci gaba da bayyana cewa, ya kamata su kasance cikin shiri tsaf yayin da suke karbar sabbin ayyukansu ta hanyar sanya hannayensu don tunkarar kalubalen siyasa da jihar ke fuskanta don juya akalar samun ci gaba .
Shatiman na Sokoto ya tunatarwa da manyan sakatarorin cewa gwamnati da jama’ar jihar suna sa ran su kawo iliminsu da dimbin kwarewar da suke da ita yayin aiwatar da manufofin gwamnati da shirye-shiryen ci gaban jihar.
A jawabin sa na godiya a madadin wadanda aka nada, Honorabul Habibu Yuguda ya godewa Gwamnan bisa daukosu da akayi , ganin sun cancanci gudanar da irin wadannan ofisoshin, sannan yayi alkawarin ba zasu yi kasa a gwiwa ba ga Gwamnan musamman a kudurin sa na ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a jihar.
Ya yi alkawarin cewa za su taimaka wa Gwamnan a yakin da yake yaki da ‘yan ta’adda da sauran munanan halaye don amfanar da jihar Zamfara da tabbatar da burin gwamnan na samar da Sabuwar Zamfara.
Sabbin mashawarta na musamman sune Hashimu Mohammed modomawa,
Sani Danjuma Dambo, Sani M. Shehu Dakko, Habibu Yuguda da Dahiru Muhammad kura.
Sauran wadanda aka rantsar a matsayin Sakatarorin din-din-din sun hada da Mainasara Shehu Bakura, Musa Liman Shinkafi, Lauwali Mainasara Bungudu da Tukur Garba
.