GWARZON DA YA KARE MAHAIFIYARSA
DAGA HARIN BARAYIN SHANU
Daga taskar labarai
Harin da barayin shanu suka kai jiya a kauyen yasure da ke kilomita biyu daga garin batsari jahar katsina ya haifar da wani gwarzo da ake labarinsa Ko ina a yankin, mai suna Muntari.
Wakilan taskar labarai sun je garin a yau jumma a don ganin irin barnar da ta faru a garin ,wakilan sunga yadda barayin shanu sukayi wa garin kar kaf.sun kwashe masu duk wani abu mai amfani.sun kuma kashe mutane uku.
Da maharan suka iso garin suna bi gida gida,sai suka zo gidansu wani matashi,Dan kasa da shekaru ashirin,mai suna muntari yana waje.sai ya dauki adda ya nufi dakin da MAHAIFIYARSA take, ya labe a bayan kyaure yasha alwashin ba Wanda ya isa, ya kai wajen MAHAIFIYARSA sai in baya da rai.
Barayin da sun yunkurin shiga dakin da take,sai ya fafaro su da adda.sai su koma gefe daya suyi ta ruwan harsashi.ga dakin
Suna harbin dakin ,amma cikin ikon Allah harsashi ko daya bai same shi ba.bai kuma samu MAHAIFIYARSA ba.
Har Mahaiflyar mai suna Rahane,tana cewa ka kyale su,su shigo dakin duk abinda zasuyi suyi.
Yace a a a.Mama sai dai in bani numfashi.
Bayan anyi wannan korar kora kamar sau uku.sai daya daga cikin maharan yace .ku kyale yaron nan MAHAIFIYARSA yake karewa.don kar a taba ta.yana bata mana lokaci,kuma yana tayi mana asarar harsashi.
Hoton harsashin da kuke gani,tare da wannan labarin. A dakin MAHAIFIYAR aka tattaro su.wakilan taskar labarai suka dau hotonsu.
An farfasa dakin da harsashi, amma Allah ya tsare muntari da MAHAIFIYARSA.