HALIN KO IN KULA DA BUHARI YA NUNA MA JIHAR KATSINA

0

HALIN KO IN KULA DA BUHARI YA NUNA MA JIHAR KATSINA

Jihar katsina itace jihar shugaban kasa Buhari, kuma itace ta ukku a Nigeria wurin bashi kuru’u masu yawa a zaben 2015 Wanda ya kaishi wannan matsayi da yake Kai.
Amma Buhari bai nuna ma jihar katsina Kulawa ba a matsayin sa na dan jihar musamman sadda wasu abubuwa suka faru kamar haka:
*1- Rasuwar Alh Lawal kaita*, tsohon gwamnan jihar kaduna kuma daya daga cikin manyan mutane a kasar nan, amma Buhari har yau bai jajanta ma iyalan sa da Al’ummar jihar mu rasuwar sa ba, balle yazo ta’aziyya duk da yana zowa jihar sai dai ya wuce Daura.
*2- Rasuwar Alh Ibrahim kumasi*, tsohon sufeton yan sandan kasar nan, kuma Abokin Buhari tun na yarinta, amma har inda ake bai je ya jajanta ma iyalan sa da Al’ummar wannan jiha ba duk da damar da ya samu ta zuwa jihar bayan rasuwar sa.
*3- Rasuwar Alh Idi Zamfare*, Wanda tarihin siyasar Buhari ba zai cika ba sai ka hada da shi, saboda irin jajircewar da yayi masa, ya kashe kudin shi saboda Buhari, Adawar da yayi saboda Buhari na cikin sababin da Allah ya sanya na karayar arzikin sa ta hanyar rufe duk hanyoyin da yake neman kudin sa da gwamnatin tayi. Wannan bawan Allah ya dau tsawon lokaci yana faman rashin lafiya amma Buhari bai iya kulawa da shi ba, sannan ya fadi ya mutu bai zo gaisuwa ba balle ya tallafa ma iyalan sa duk da shi Idi zamfare babu abinda bai ma Buhari da kudin sa ba.
Miye amfanin zuwan Buhari katsina a ranar Alhamis domin kamfen bayan baiyi ma mutanen katsina halacci ba.
In yazo me zai gaya mana?! Wane aiki yayi ma jihar da zai fada?! Gidan yarin da ya gina wanda shi kadai ne aikin da ya kirkiro har ya gama a hanayar jibiya?!
Koko gaisuwar wadannan bayin Allah zai mana yanzu?!
Koko maganar satar mutanen da akeyi wadda bata ma dame shi ba balle ya dauki mataki?!.
Allah ka zaba mana shugabanni na gari masu tsoron ka da tausayin talakkawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here