HALIN TSARO KATSINA NA TSAKA MAI WUYA……ZAMFARA CE MATSALARMU

0

Shahin Katsina City News

 

Jihar Katsina na daya daga cikin yankin da ke tsaka mai wuya a mummunan halin tsaro daga ‘yan bindiga masu kisa da satar mutane a Arewa maso Yamma da kuma kasar nan.

 

Jihar Zamfara, wadda ita ce kanwa uwar gamin matsalar tsaron ‘yan bindiga da sunan sulhuntawa saboda zaben 2023 da wadannan ‘yan bindigar.

 

Mafi yawan yarjejeniyar tana kamawa ne kamar haka. Ku kyale dajin Zamfara da mutanenta, amma duk inda kuka je ba ruwanmu.

 

Daga wannan yarjejeniyar da Zamfara ke yi da ‘yan bindiga, yanzu wadannan ‘yan ta’adda kamar sun samu mafaka a hukumance.

 

Masana tsarin yaki sun tabbatar babu yakin da za a iya nasara idan makiyinka yana da mazauni a kofar gidanka.

 

Wadannan ‘yan ta’addar suna dauke da makamansu suna watayawa yadda suke so a yankin.

 

Sun zama kamar wasu sojojin haya, abokan ta’addancinsu suna gayyatarsu aiki a wasu jihohin su yi su dauki kasonsu su koma.

 

Wadda ta fi wahala daga wannan mummunan yanayi ita ce Jihar Katsina.

 

Abin tsoro shi ne nan gaba a fara daukar hayar wadannan ‘yan ta’addar daga daji don aiwatar da kisa ko kashe-kashe don siyasa.

 

Saboda yanzu suna kara zamanatar da ta’asar tasu a matsayin neman kudi da rayuwa a kan wannan.

 

Wani lamarin kuma shi ne majiyoyinmu sun tabbatar wa da jaridunmu cewa, gamayyar jami’an tsaro sun yi wa duk wani sansanin ‘yan ta’adda da ke kusa da babban titin Kaduna zuwa Abuja raga-raga.

 

‘Yan bindigar yanzu sun tarwatse zuwa can cikin daji. Wannan ya sanya suka dauki lokaci ba su yi hari ba, domin sai sun yi doguwar tafiya.

 

An takura su a dajin da yawan harin. Wadannan miyagun yanzu wasu sun koma bangaren Birnin Gwari, wasu Zamfara wajen ‘yan’uwansu da suke da fahimta da gwamnatin Zamfara da wasu dazuzzukan Katsina.

See also  ZABEN FIDDA GWANI NA APC: Me Ya Faru A Zaman Sulhun Da Aka Yi? 

 

Wadannan gudaddun masu dauke da makamai duk lokacin da kwayarsu ta motsa, Jihar Katsina ce mafi kusa su murza guminsu.

 

Katsina na da iyaka da kasar Nijar, jami’an tsaron Nijar ba su yi wa ‘yan bindigar nan da dadi.

 

Don haka kullum mafakarsu su shiga Zamfara wajen ‘yan’uwansu masu fahimta da gwamnati in sun huta su shigo Katsina su yi ta’addaci.

 

Majiyarmu a hukumomin tsaro sun tabbatar wa da jaridun mu cewa, har yanzu ‘yan bindigar nan na da wani shiri na kai wa babban birnin Katsina wani hari da zai girgiza Jihar da Kasar baki daya.

 

Ana kitsa shirin ne daga dajin Zamfara. Wani kasurgumin dan ta’adda da ke da fahimta da gwamnatin Zamfara shi ne ake zargin yake jagorantar shirin.

 

Kodayake hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana wajen hana aukuwar hakan. Suna tattara bayanai da kuma katse masu hanzari.

 

Mene ne mafita? Ta farko, ita ce addu’o’i kala-kala wadda Allah zai ji tausayinmu.

 

Na biyu, kafa jami’an tsaron kare kai na garuruwa, unguwanni da shiyya. Kowa ya shigo ciki. Wani ya ba da karfin sa, wani kudi, wani addu’a. Kowa ya ba da irin tasa gudunmuwar da zai iya.

 

Na uku, mu yi fata da addu’a da goyon bayan wani tsarin tsaro da gwamnatin Jiha take son bullo da shi ya yi nasara.

 

Shirin yanzu haka an ware masa kudi da tsari, kuma har Majalisar Jiha ta amince da shi. Wata runduna ce za a kafa da duk hukumomin tsaro da kuma na kungiyoyinsa kai.

 

Na hudu, kar ku dogara ga jami’an tsaro su kawo maku dauki. Ku fada wa jami’an tsaro kuna cikin hari, amma ku kare kanku.

 

Katsina City News

@ www.katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

@ www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here