Daga Ibrahim Hamisu, Kano
@ jaridar taskar labarai
Hassanal Bolkiah ne sarki, Yang di-pertuan kuma Fira Ministan daular Brunei, wanda ya sanya ya zamo ɗaya daga cikin hamshaƙan sarakuna na yanzu. Yana da manyan motocin alfarma guda 7,000 a cikin garejinsa.
Daular Brunei ƙasa ce mai iko da ke gaɓar tekun arewa na tsibirin Borneo a gabashin nahiyar Asia. Bayan sarauta, ya kasance mai matuƙar son tsadaddun motocin alfarma wanda ya sanya ya tara motoci dubu bakwai a cikin garejinsa.
Ga jerin kalolin motocin:
Kirar Rolls Royc 604
Kirar Mercedes Benz 574
Kirar Ferrari 452
Kirar BMW 209
Kirar Jaguar 179
Kirar Coenigsegg 134
Kirar Lamborghini 21
Kirar Aston Martin 11
Kirar SSC 1
Rahotanni sun tabbatar da cewa dukkanin motocin harsashi bai iya huda su, kamfani Marsidi ya kera masa wata mota ta musamman, wanda hakan ya nuna duk duniya babu mai irin motar sai sarki Hassanal Bolkia, haka kuma sarkin yana da lambar mota Marsidi Benz da aka kerata da zinari,
Da wannan adadin 450 na kirar Ferrari da sarki ya ke da su, Sarkin Hassanal ya zama shi ne na farko a duniya da ya ke da wannan Kaloli na Ferrari.
Saboda jin dadin da ya ke na son hawa tadaddun motoci, hakan ta sa ya baiwa maaikatansa umurni da su ajiye masa motar nan kirar Rolls Royco a gaban fadarsa awa 24 a kunne, gudun kar a bata masa lokaci ya yin da yake son fita da gaggawa.
An kiyasta cewa kudin motocin zai kai dala biliyan 20, Hassanal dai yana da ‘yaya maza guda 5 da mata guda 7.
@ jaridar taskar labarai. Www.taskarlabarai.com