HARE HARE A SABUWA DA FASKARI
Muazu hassan
@ taskar labarai
Mafi yawan gonakin yankin sabuwa da faskari an noma su, don haka ba za a samu matsalar abincin noma mai muni da ake tsammani ba. Sai dai a wasu gonakin manoma na tsare gonakin su daga mahara.
Duk da haka a wadannan yankunan har yanzu mahara na kai harin neman kudi, kayan abinci da dabbobi.
A cikin satin nan dake karewa mahara sun kai Hari a ranar litinin 24/8/2020.inda suka je garin mararrabar mai gora.,yankin machika suka kwashi kayan abinci da kuma wani mutum daya.
A kuma ranar 27/8/2020 wasu maharan sunje yar kaka, yankin gazari suka tafi da shanu takwas,suka sari wata mata da tayi masu gardamar su debi abincin ta.suka kuma tara wasu mutane sukayi ta bugu.suna zaginsu da fada masu miyagun maganganu.
An fada ma taskar labarai cewa, ana shaida ma sojoji suka kawo dauki.wanda wannan ya taimaka maharan suka gudu ba tare da sun tafi da kowa ba.
A kuma daren jumma ar nan maharan sun shiga unguwar Haji dake karamar hukumar faskari. Sun kwashi abinci sun kuma tafi da mutane biyar.
Rundunar sojan da ke yaki da wadannan miyagun ta shaida wa manema labarai cewa. A sati daya sun kama mahara da masu hadin baki dasu.da yawan gaske.
Sun kuma kwato makamai da shanu daga wajen su.sun kuma jaddada cewa a shirye su kai dauki ga duk wadanda suka basu Rahoto ingantacce na wadannan yan ta addar.