HARI A SABUWA

0

HARI A SABUWA
muazu hassan
@ taskar labarai
Mahara daga daji na ci gaba da matsama bayin Allah a karamar hukumar sabuwa.wakilanmu sun tabbatar da hare hare a garuruwa kamar haka.
Ana gama sallar Isha I. Maharan sun kai farmaki a ranar litinin 24/8/2020 a garin maigora machika wad.sun kwashi kayan gona sun kuma tafi da mutum daya.a kuma ranar, wasu barayin sunje garin Dandume, karamar hukumar Dandume unguwar danbaba, sun tafi da wata mata guda daya.sun kuma je wani gari mai suna Awala dake karamar hukumar sabuwa.sun tafi da mutane hudu.
Jaridar nan ta gano kauyuka, ar ba in, wadanda basa kwana a gidajen su. In dare yayi sai dai su kwana a cikin daji suna gadi.kauyukan sun hada da sayau , rafin tsiwa,sayau tasha da sauransu. Duk a karamar hukumar sabuwa.
Hare hare sun yi sauki a wasu yankunan na katsina.misali jibia, batsari, safana,Dan Musa, kurfi da Dutsinma. Duk lamarin ya lafa.sai abin da ba a rasa ba.
Amma yankunan sabuwa, faskari, Dandume har yanzu maharan na kai Hari akai akai. Sai dai soja dake aiki a yankin suna fadawa manema labarai cewa sun kusa cin lagonsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here