HARKA TSARO A JIHAR KATSINA: WA YA GAZA?

0

HARKA TSARO A JIHAR KATSINA: WA YA GAZA?

Tare da Abdulrahman Aliyu

@Taskar Labarai

A Lokuttana baya jihar Katsina muna jin labarin matsalar tsaro ne kawai a wasu kasashe da suka shahara kan rikincin kabilanci ko kuma rikicin neman mulki mai nasaba da kabilanci. Irin su Saliyo, Burundi, Makawi, Libiya da sauransu.

Matsalar tsaro a jihar Katsina ta fara ne a yankunan da ke zagaye da dajin rugu, irin su Safana, Faskari, Kankara, Batsari Jibiya, Sabuwa da sauransu.

Asalin abun za a iya cewa ya fara ne tsakanin fadan makiyaya da manoma, wanda yawanci fadan kan faru ne a shekara-shekara gaf da kammala kauda amfani gona. A lokacin babu bullar makamai na zamani sosai ana amfani da wukake ne da kanana bindigogi.

Ko shakka babu a lokacin ta’azzarar rikicin akwai zargi da yawa da ke nuna hannun uwayen kasa a cikin sa, wanda ake zarginsu da amsar na goro daga wajen Fulani domin sakin su ko kyale su idan sun aikata laifuka. A lokacin gwamnati bata cika tsoma bakinta a ciki ba, su wadannan uwayen kasar suke da alhakin tabbatar da yin sulhu a tsakanin makiyayen da manoman.

Akwai misalai da yawa da za a iya kawowa na hannun wasu daga cikin uwayen kasa kan ginuwar wannan annoba da ta girma a yanzu.

Bayan da makamai suka yawaita a hannun mutane musamman bayan kammala juyin-juya halin Libiya, wanda ya taimaka wajen yaduwar makamai a wasu sassa na Nijeriya baki daya.

Sai wadannan Fulanin suka fara yakar junansu, suna kwashe shanun ‘yan uwansu ta amfani da karfi, a lokacin sauran al’umma da gwamnati basu dauki abun da wani tasiri ba, asali ma dariya ake ana nuna cewa ai su ci kansu.

Lokacin da suka karar da junansu kowa ya koma dan bindiga a tsakanin su, sai suka sauya dabara, suka rika kama mutane domin su karbi kudin fansa, shima sun fara ne tsakanin su, aje har gidan wanda aka fi karfi a kamo shi, sai ya biya. Daga baya kuma sai suka rika kan mai uwa da wabi.

Gwamanti bata dauki abun da wani muhimmanci ba a lokacin, duba da cewa ba a taba wani babba mutum ko kuma wani jami’inta, wanda hakan ya taimaka wajen girmamar abun. Wani abu da zai baka haushi yadda a nan Katsina wani baban uban kasa ya danganta abun da laifin talakawa, wai me yasa ma suke bada kudin, ai suke ma zuzuta abun da suke bada kudi, bai taba tunanin abun zai kai ga kashe mai hakimi ba. Wanda radadin abun ga wanda aka yi ma wa ba wata mafita sai biyan, ko kuma mutuwa.

A gefe guda kuma su jami’an tsaron dama can wajen daukar su aiki bara gurbin al’umma ne aka dauka matsayin kananan jami’an tsaro, domin sanin kowa ne a lokuttan baya duk wanda aka ga ya tafi kurtun soja ko Dansanda, ana masa kallon wanda ya rasa yadda zai yi ne kawai a cikin al’umma. Tsiraru ne ke tafiya da niyyar bautatawa kasa.

Wannan tunanin ya taimaka kwarai wajen daukar gurbatattun jami’an tsaro, wanda suna hadin kai ne da su wadannan ‘yan bindigar domin ana ware masu kason su.

Akwai misalin irin wannan da yawa, an kama jami’an tsaro da yawa da hannu wajen sayar wa ‘yan bindaia harsashe da makamai kai kwanakin baya har sojoji aka samu sun tare jami’an ‘yansanda sun tsairatar da wani kasurgurmin dan ta’adda saboda kawai abin da ake basu.

Za ka sha mamaki in kaje Batsari ko wasu yankuna da abun ke faruwa kaga manyan mutanen da ke alaka da wadanan mutane, wanda su a wurinsu suna ganin cewa alaka da wadanann mutane kariya ce garesu.

See also  YADDA 'YAN BINDIGA SUKE CIN KARENSU BA BABBAKA A BATSARI

Matsala ta gaba ita ce rashin ingantattun kayan aiki da ba a ba jami’an tsaron saboda wasu daga cikin manyan basu bukatar a gama wannan abu sakamakon abun da suke samu, wanda suke ganin da an gama wannan abu kamar samayyarsu ta kare. Akwai misalan haka da yawa, duba da cewa an samu manyan jami’antsaro a kasar nan da irin wannan ta’annati.

Idan muka koma a bangaren gwamnatin jihar Katsina kuwa, tana da babban laifi musamman ganin cewa wanann matsala gadar ta tayi. Sulhun da ka yi a gaskiya kuskure ne, domin ba a sulhu da wani kaso a kyale wani, in zaka yi sulhu kabi irin tsarin da aka bi a yankin Neja Delta. Ba wai kayi sulhu da wadanda ka sani ba kuma kake so ka kyale wasu.

Kuma saboda tsananin rauni wai har ka rika gayyato wadannan mutane a fadar gwamnatin jiha, suna ganinku cikin daula da wadata, su kuma suna can suna ‘yar tsere tsakaninsu da ‘yan uwansu ‘yan ta’adda a cikin daji.

Haka kuma, gwamantin jihar Katsina gwamnati ce ta al’umma wadda al’umma suka zaba, amma kowa ya sani a bangaren tsaro ba a bada dama ga mai ba gwamana shawara ba a bangaren tsaron wanda shi kwararre na a fannin amma saboda son rai sai aka yi watsi da shi, wanda wanann kadai ya isa ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin jihar kamar ba da gaske take ba.

Ita kuwa gwamnatin tarayya dama bata jihar Katsina take ba, domin gani ma suke kamar ‘yan jarida ne ke zuzuta matsalar shi yasa kullum matakin a baki yake kawai ba a aikace ba.

Tarihin ta’addanci da yake-yake a duniya ya tabbatar da cewa duk kasa ko yankin da ya samu kansa cikin irin wannan halin. To yana da zabi biyu ne kacal.

Zabi na farko ko dai su al’umma su zama jami’an tsaron kansu, su nada kwamitoci na sirri da amintattu wadanda zasu rika sanya ido kan shige da ficen mutanen cikinsu tare da bibiyar duk wani da ba a yadda da motsinsa ba koda kuwa uban kasa ne.

Haka kuma, sai al’ummar ta cire tsoro da ta fuskanci wadannan ‘yanta’adda ta amfani da yawa da kuma nau’in makaman da ke hannunsu koda basu kai na su wadancan abokan gabar ba su fuskanta wa Allah kome. Irin haka ne ta faru tsakanin Musulmi da Kafurai a yakin Badar, kuma Allah yaba Musulmai nasara duk da cewa su kafuran ma sun linka Musulman sau uku da doriya tare da fin su tarin makamai.

To amma saboda zaluncinmu da kin gaskiyar mu da matukar tsoron mutuwa, dole ne wadannan bala’o’i su rika haye mana, bambancin mu da ‘yanta’addai kadan ne. ‘Yan kasuwar mu macuta, malamanmu makwadaita, mawadatanmu azzalumai shugabaninmu maha’inta, talakawanmu magulmata mahassada, dole ne Allah ya jefa tsoro a zukatanmu, mu koma kona Bilbod madadin tunkarar ‘yan bindiga domin nemar wa kanmu mafita.

Mafita ta biyu ita ce mu yi hijira daga inda wadannan Yan bindigar suke mu tashi mu yi gaba, tunda ba yadda zamu yi sai gwamnati ta magance mana su mun dawo.

Daga karshe dai muna addu’ar Allah ya kara mana kwarin guiwar tunkarar wadannan ‘Yan ta’adda da karfin mu ya kuma bamu nasara a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here