Rahoton musamman
@Katsina City News
Jaridun Katsina City News, sun yi bincike a tsakanin ’yan takarkarin Gwamna da ake da su a kan su wa suka tallafa wa jami’an jam’iyyarsu da wadanda ke masu wahala?
Bincikenmu ya gano wanda jam’iyyar PDP ta tsayar takara, Alhaji Yakubu Lado Dan Marke, ya yi wa masu rike da mukamai a jam’iyyarsa da wasu ’yan takarkarin, kamar na Majalisar Jiha, Tarayya da Sanata, har da ma da Shugabannin Kananan Hukumomi hasafin abin da za su yi Sallah da shi.
An tabbatar mana yadda aka raba kudin, wanda har wasu jaridun yanar gizo sun rubuta labarin, ciki har da Katsina City News.
Mun gano dan takarar jam’iyyar NNPP, Injiniya Nura Khalil, shi ma ya duba wa wasu daga jami’an jam’iyyar da wasu muhimman ’yan jam’iyyar tasa, ya ba su na cefanen Sallah. Duk da ba a yayata yadda ya raba nasa ba, amma wani babban jami’in jam’iyyar ya tabbatar mana, har da wadanda suka amfana.
Shi kuma dan takarar Gwamna a jam’iyyar SDP, Alhaji Ibrahim Zakari Ibrahim, ya yi rabon kudin cefanen Sallah ne ga tsaffin abokan siyasarsa.
Ba mu da tabbacin ko ya ba ’yan sabuwar jam’iyyar da suka ba shi takara wato SDP, amma mun samu tabbacin ya bai wa abokan siyasarsa a Karamar Hukumarsa ta mashi da kuma Katsina.
Haka shi ma dan takarar Gwamna a jam’iyyar ADC, ya raba wa abokan siyasarsa da kuma wasu jami’an jam’iyyar hasafin Sallah, kamar yadda na kusa da shi suka tabbatar wa jaridun nan.
Mun kasa samun tabbacin ko dan takarar jam’iyyar PRP, shi ma ya bayar da na cefanen? Wayoyinsa ba sa shiga, kuma ba ya da wanda ke magana a madadin shi, ofishin jam’iyyar na Jiha, kuma kullum a kule yake. Babu maigadi, balle masinja, ko mai amsar takardu.
Dan takarar babbar jam’iyya mai mulki, wato APC, Alhaji Dikko Umar Radda, bincikenmu ya gano ko Sisi bai bai wa jami’an jam’iyyarsa ba, balle wasu manyan abokan siyasarsa, ko kuma wasu yaransa da suke masa wahalar siyasa. Kamar yadda suka tabbatar mana bisa amanar kar mu kama
sunansu. An ce ya yi tafiya zuwa Kasa Mai Tsarki don aikin Hajji, kuma bai bar wani shiri na yin hakan a kasa ba.
Mun yi kokarin jin dalilin haka, ta ofishin jam’iyyar APC. Wani jami’in da bai son a ambaci sunansa ya ce, wannan magana ce ta dan takara, ba ta jam’iyya ba. Ya ce har yanzu dan takara shi ne ke tsara harkokinsa. Don haka a nemi dan takara.
Mun kasa samun wanda zai yi magana a madadin dan takarar domin ofis din kamfen dinsa da ke kusa da shataletalen Kofar Marusa, duk zuwan da muka yi a kule yake, ba kowa. Wayar jami’in kamfen dinsa duk kira a kule take.
Tambayoyin da ke yawo a Katsina, me ya sa duk da shi ne ya yi nasarar samun tikitin APC, kuma jam’iyyar da ke mulki a Katsina yanzu ta kyale ’yan jam’iyya da wasu mutanensa na siyasa da wasu yaransa a lokacin Sallar Layya?
Me ya sa lokacin zaben fitar da dan takarar ya fitar da kudin yakin neman zabe kamar hauka?
Me ya sanya babu wanda zai iya yi masa hidimar Sallah ga mutanensa, ko da a bayan idonsa ne?
Bincikenmu ya gano wasu ’yan takarkarin da suka fadi zabe a neman Gwamna a APC sun yi wa mutanensu hidima.
Mataimakin Gwamnan Katsina, Dattijo Alhaji Mannir Yakubu, duk hidimar da yake wa ’yan’uwa da abokan siyasarsa, da mutanen arzikin dake tare dashi,ba wanda ya tsaya a hidimar Babbar Sallah.
Tsohon Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa shi ma babu abin da ya fasa.
Kwamishinan Kasafin da Tsare, Alhaji Farouk Jobe, shi ma ya yi wa mutanensa cefanen Sallah.
Haka Alhaji Abbas Masanawa da kuma Sanata Saddiq ’Yar’adua, ya rabar da danyen abinci da kudi.
Ko me wannan ke nunawa? Wannan ita ce tambayar da mutane ke yi a kan ’yan takarkarin a Jihar Katsina.
Katsina city news
@www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245
Email;newsthelinks@gmail.com