HON. ARMAYA’U ABDULƘADIR YA BADA TALLAFIN KUJERU 180 GA MAKARUNTU
Daga Abubakar shafi’i Alolo
Hon. Armaya’u Abdulƙadir Danmajalissa mai wakiltar Dutsin-ma/Kurfi ya raba kujeru guda 180 gudummuwarsa ga Makaratun Scondary School don inganta karatun al’ummar yankinsa da yake wakilta.
An kaddamar da wannan rabon kujeru a Pilot Day Secondary School Dutsi-ma.
Wakilan Hon. Armaya’u Abdulkadir sun damƙa wannan kujeru ga hannun Zonal Education Director Mal. Idris Isah Birchi don rarraba wannan kujeru ga makaratun da su kafi buƙata da sauri a cikin ƙaramar hukumar Dutsin-ma. Wannan farko ne aka fara. Zuwa na gaba za’ayi wannan program a Ƙaramar Hukumar Ƙurfi.
L.A Hon. Abdulhadi Bala Karofi shi ne ya wakilci Hon. Armaya’u Abdulƙadir ya bada wannan Kujeru tare dashi da Malam Ibrahim Bature Dutsin-ma, Sun gudanar da jawabi a madadinsa na yanda za’a raba kujerun.
1) Government Pilot 40Chairs
2) Government Day Secondary 40Chairs
3) Community College Of Arabic and Islamic Studies 30Chairs
4) Community Day Secondary Dutsin-ma 30Chairs
5) Government Day Girl Secondary 30Chairs
Ya kuma bada tallafin kudi ga masu sana a.dama yana bada magani ga masu cutar sikla duk karshen wata
Nan gaba kadan za a ba wasu makarantun a karamar hukumar Kurfi. Kamar yadda aka yi a Dutsinma
Wanda ya rubuta
Abubakar Shafi’i Alolo
Wanda ya tace Abdurrahaman Aliyu