Daga Abdulrahaman Aliyu
Honorable Sani Danlami ya na daga cikin Matasan ‘yan siyasa da suka taso da farinjini a wurin jama’a.
Tun kafin ya kai bisa wannan kujerar Sani Danlami mutum ne jajirtacce mai akidar siyasa, wanda duk wani wanda ke wakilin Kudu 3 ya san irin gwagwarmayar da ya yi tun a jam’iyyar APP/ANPP har zuwa CPC, kafin ayi maja ta koma APC. Sani Danlami ya sha gwagwarmaya matuka da yan jam’iyyar PDP, kai wasu ma sun ce a filin ATC har sumar da shi an taba yi, amma kuma bai sauya ra’ayinsa ba.
Bayan da gwamnatin APC ta ci zabe a 2015 an kyautatawa Hon Sani Danlami zato musamman irin kusancin da ake ganin ya na da shi da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari. Wasu sun kyautata zaton a lokacin za a iya bashi kwamishina ko kuma wata kujera mai maski.
Kwatsam sai mutuwa ta daka wawa ga Danmajalissar mai wakiltar karamar hukumar Katsina a Abuja Hon. Shak Umar.
Matasa da wasu masu kishin jihar nan sun wo ca kan Sani Danlami ya fito ya nemi wannan kujera, an ce kafin ya amince sai da ya tuntubi mutane da dama wadanda ya ke tunanin za su iya neman kujerar, sai suka yi masa fatan alheri ya tafi ya nema.
Sani Danlami ya samu sa’a ya ci zaben fitar da gwani wanda cikin wadanda ya kada har da tsohon dan takarar Gwamna Alhaji Abdul’aziz Musa (Abdu Soja). Sannan kuma a babban zabe ya yi nasarar kada Dan takarar PDP, wanda shi ma da ne ga Marigayi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman.
Wannan nasara ta sanya talakawa sun ta kururuta wannan dantakara a matsayin nasu ya samu, duk da irin sukar da ya sha ta bai iya Turanci ba da karancin ilimin boko da ake mai gorinshi.
Da farko Sani Danlami ya zama fitila a cikin fitilu saboda yadda ya fara ayyukan alheri da taimakon marasa karfe da kyautatawa, har ta kai ana masa lakabi da mai raba alheri. Ya tashi tsaye wajen ganin ya yi ayyukan cigaba a mazabarshi, wadanda za su taimaki al’ummarsa, ya fara gina bohol-bohol da samar da magunguna ga asibitoci da tallafawa marasa lafiya da sauran ayyukan alheri, ana ta yabonsa.
Ashe karin maganar nan ta Bahaushe da ya ce “Tsiyar Nasara sai za ya gida”. Cikin kankannin lokaci Sani Danlami ya sauya tunaninsa, ayyukan da ya kamata ya yi ya ki yi, ya koma tara yanbangar Siyasa da yan bambadanci a kafafen yada labarai, Karya da saba alkawari irin na Yansiyasa suka zama jininsa, ya watsar da duk wadanda suka taimaka mashi ya rungumi masu yi mashi hudubar Shaidan.
A zahirin gaskiya in aka yi la’akari da ayyukan da wasu masu rike da irin kujerunsa ke yi to sai muce shi ya zama mai dumama kujera kawai a Abuja.
Duk da ban da masaniya ko Honorable Sani Danlami ya na bukatar tazarce ko baya bukata, amma dai ya kamata ya san cewa kujerar da yake bisa yanzu ba ta din-din bace, sannan ya zuwa yanzu mutanen da ke neman kujerar da gaske suke, kuma da yawa daga cikinsu za su iya karbar kujerar a hanunsa cikin ruwan sanyi.
Isah Barda ya na daya daga cikin masu neman wannan kujera kuma ya zuwa yanzu alamu na gwada ya samu karbuwa a wajen mutane, musamman irin taimako da kuma ayyukan da yake gudanarwa a karkashin ofis dinshi. Don haka barazana ce babba ga kujerar Sani Danlami. Sannan shi ma ya na da kusanci da gwamana sosai, musamman ma kasancewar babansa ne ya ba Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari mukamin kwamishina lokacin da ya yi gwamana, akwai yiwuwar Shima Gwamna ya Saka mai.
Sadiq Ayuba Sullubawa, duk da cewa ba wani fitaccen dan siyasa ba ne, amma yadda matasa suka rungume shi da kuma irin ayyukan Jin kai da yasa gaba, za su iya taimaka mashi wajen ganin ya samu wannan kujer ta Majalissar Tarayya a karamar hukumar Katsina.
Dr Ahmed Adamu matashin Malamin Jami’a kuma masanin tattalin arziki, kwararre da ya rike mukamai da dama a fadin kasar nan da ma duniya baki daya kan abin da ya shafi Jagorancin Matasa. Shi ma wannan wani kalubale ne da zai iya zama barazana ga Kujerar Sani Danlami, musamman ma kasancewar taken zaben bana ana kallon cancanta za a duba ba jam’iyya ba.
Irin yadda matasa da Yanboko ke goyan bayansa ana kyautata zaton zai iya kai labari a 2019.
Wadannan mutane uku ya zuwa yanzu kusan sune za su iya zama barazana ga Sani Danlami.
Har zuwa yanzu Hon, Sani Danlami zai iya gyara kura-kuran da ya yi musamman ma ganin akwai shawarwari da kwararru suka bashi kuma ya na da su a hannunsa, ya na iya diba wadannan shawarwari domin kara ma dabensa makuba.
2019 dai kowa tasa ta fissheshi.