Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Shugaban hukumar zaben jihar Kano, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar KANSIEC ta sanya ranar 16 ga watan Janairun shekarar 2021 a matsayin ranar da za’a gudanar zaben ƙananan hukumomin jihar.
Farfesa Garba Ibrahim Sheka shi ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a shalkwatar hukumar.
Jihar Kano dai na da kananan hukumomi 44, fiye da kowacce jiha a fadin kasar nan.