Hukumar Kwastam ta kama mazakutar jaki 7,000 da ake shirin fita da su waje

0

Hukumar kwastam a Najeriya ta ce ta yi nasarar hana fita da mazakutar jakuna 7000 da aka yi shirin safarar su zuwa Hong Kong.

 

Kwastam ta yi wawan kamun ne ranar Laraba a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke birnin Lagos.

 

Kwantirola mai kula da filin jirgin sama Sambo Dan Galadima ne ya tabbatar da hakan a tattaunawarsa da BBC ranar Laraba, yana mai cewa an nade mazakutar jakunan ne a cikin buhunhuna 16.

 

Dan Galadima ya kara da cewa wadanda ake zargi da yunkurin safarar kayan sun tsere daga filin jirgin, a lokacin da jami’an kwastam suka nuna shakkun kan abin da ke cikin buhunhunan, sakamakon warin da ya turnuke wurin lokacin binciken kayan.

See also  Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma APC a Jihar Gombe

 

Darajar kayan dai ta kai sama da naira, 216,212,813.58.

 

Najeriya ta haramta safarar fatu ko duk wani abu da ya shafi jaki zuwa kasashen ketare, sakamakon karancinsu da ake fuskanta a kasa.

 

Kasashen yankin Asiya kamar China, yankin Hong Kong, da Koriya ta Kudu, da sauransu, na amfani da shi wajen yin magungunan gargajiya.

Majiya: daily Nigerian hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here