Hukumar Sojin Najeriya ta sallami daya daga cikin jami’anta, Ibrahim Abdullahi, daga aikin aikin Soja bisa laifin sata, Jaridar SaharaReporters ta ruwaito.
Ibrahim Abdullahi wanda Lance Kofur ne yana aiki a makarantar sufuri ta hukumar Soji Nigerian Army School of Supply and Transport (NASST), dake Ugbowo, Benin City, jihar Edo, gabanin sallamarsa.
An sallamesa ne ranar 8 ga Satumba, 2022 kan laifukan damfare-damfare da yawa.