HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA KANO ZA TA TANTACE MASU YABON MA’AIKI S.A.W

0

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA KANO ZA TA TANTACE MASU YABON MA’AIKI S.A.W

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar ta ce finafinai ta jihar Kano, ta ce za ta tantance dukkanin masu yabo na jihar Kano, ganin yadda wasu ke wuce kaida da fadin maganganun da ba su da ce ba a da sunan wake,

Shugaban hukumar ta ce Finafinai ta jihar Kano Ismaila Na’abba Afakallah ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Freedom Radiyo kano, inda ya ce an kafa kwamiti da zai tantance kuma ya yi masu rigista kafin su saki waka ko su rera a jihar kano,

Ya kara da cewa ” Ba yadda zaa yi a bar mutane su ta fi kara zube, suna wake waken da zai tunzura jamaa ko kuma ya kawo fushin Allah, don haka lallai hukuma ta tsaya da zarar an dawo daga hutun dole, ba wani mawaki da zai yi bege a jihar Kano sai yana da lasisi da hukumar ta ce Finafimai sai an tantane shi, sannan babu wanda zai je ya yi bege ko majalisi dole sai an bashi dama ya je yayi, duk ba don wani abu ba sai don a tsaftace harshe akan kalamai da ake wa Allah SWT da Manzo S.A.W da bayin Allah”.

See also  KASASHE GOMA DA SUKA SHAHARA WAJEN CIN ZARAFIN MATA DA YI MASU FYADE

Afakallah ya tabbatar da cewa majalisi a taron biki ko suna ko kuma mawaki zai fitar da wata waka sabuwa, dukkaninsu sai mutum yana da izini da wannan hukuma ta tace Finafinai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here