Hukumar zabe ta sanya 5/12/2020 a matsayin ranar zaben kananan hukumomi a zamfara

0

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar zamfara ta sanya ranar Asabar 5/12/2020, a matsayin ranar da zata gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.

Hakan ya fitone cikin wata takarda da aka rabata ga manema labaru,wadda ke dauke da sa hannun sakataren hukumar Muhammad Sani Halilu Kura.

Yace yin hakana ya biyo bayan umurnin da gwamnan jihar zamfara Bello Muhammed Matawalle ya bayar, cewa hukumar zaben ta tabbatar da ta shirya zaben kananan hukumomi, ba tare da bata lokaci ba.

Ya kara da cewa, Shugaban hukumar zaben na jihar Zamfara Alhaji Garba Muhammad Danburan Gusau, yana farin cikin shedawa jama’a da dukan jam’iyyun da ke da rajista , da jami’an tsaro, da kafafen yada labarai, da kuma dukan masu ruwa da tsaki cewa an tsaida ranar biyar ga watan Disamba na wannan shekara (5/12/2020),Ta zama ranar da za’a gudanar da zaben na kananan hukumomi .

See also  Za Mu Mikawa Gwamnati Motoci 48 Da Muka Bankado A Sokoto- Kwastam

Danburan Gusau ya nemi goyon bayan jama’a da masu fada aji da dai sauran masu ruwa da tsaki, domin su gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here