Khadijah Abubakar @Taskar labarai

Quantity Saveyor Alhaji Manni Yakubu ya kira taron Manema Labarai domin bayyana wa Al’umma jihar Katsina manufofin sa, da irin yunkurin sa idan Allah ya nufa ya zama Gwamnan jihar Katsina a 2023.

QS. Mannir Yakubu tsohon Kwamishinan Noma, kuma mataimakin Gwamnan jihar Katsina, a taron da ya gabatar da jawabinsa cikin harshen turanci da Hausa, a ɗakin taro na MUNAJ EVEN dake daura da gidajen Fatima Shema, ya zayyano Manufofi da Ƙudurorin sa, da kuma irin ayyukan da zai maida hankali idan Allah ya bashi Kujerar Gwamnan, idan yace idan Allah bai nufa ba ya zama Gwamna zai ci gaba da Gwagwarmaya dama ita ya saba injishi.

“Na fito Takarar Sanata, na fito Takarar Gwamna nayi siyasa tun Jam’iyyar PRP, don haka na dade ina gwagwarmaya” Mannir ya fada.

Sana Qs. Mannir Yakubu ya bayyana yanda y samu gogewa a zamansa na mataimakin Gwamna, kuma Kwamishinan Noma, sana gashi dan’kasuwa tabbas yana da gogewar da zai iya fidda jihar Katsina kunya, ta fannoni daban-daban. “A cikin wannan Gwamnatin Mun gina makarantu mun gyara asibitoci mun maida su na zamani munyi Sabbin tituna na kilomitoci, mun bunƙasa harakar Noma, da samar da ingantaccen Iri, munyi tsarin Ilimi mai kyau wanda yasa yaran mu a yanzu basa faduwa jarabawa” injishi.

See also  Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Ma'aikata Na Jihar Katsina (1}

A bangaren tsaro Qs. Mannir Yakubu ya Bayyana yanda za’a shigo da wani salo tundaga matakin unguwanni, da ‘yansandan al’uma, inda yace, Gwamna shine Shugaban tsaro na Jihar sa, amma kusani, bashi da ‘Yansanda bashi da Soja dukkanin su, suna amsar umarni ne daga sama, don haka dole su Ɓullo da wani tsari na tsaro da zai taimaki al’umma. Inji Mannir Yakubu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here