INEC TA DAGE DUKKAN ZABUBBUKA CIKE GURBI SABODA TARZOMAR END SARS

0

INEC TA DAGE DUKKAN ZABUBBUKA CIKE GURBI SABODA TARZOMAR endsars

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ɗage dukkan zaɓuɓɓukan cike gurbi da ta shirya yi a jihohi 11 na ƙasar nan.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin hukumar, Festus Okoye, ya ce an dakatar da gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabe 15 saboda halin rashin tsaro da ake ciki yanzu.

A da an shirya yin zaɓuɓɓuka shida na sanatoci da kuma tara na majalisun jihohi a ranar 31 ga Oktoba.

Zanga-zangar Allah-wadai da ta’asar ‘yansandan SARS ƙarƙashin yekuwar #EndSARS dai ta rikiɗe ta zama tarzoma wadda har da kashe rayuka a sassan ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here